Da Dumisa: Kotu a kasar waje ta sa ranar yanke shawarin mika Sunday Igboho Najeriya

Da Dumisa: Kotu a kasar waje ta sa ranar yanke shawarin mika Sunday Igboho Najeriya

  • Rahoto ya bayyana cewa, an samu labarin ranar da za a saurari karar yiwuwar mika Sunday Igboho ga gwamnatin Najeriya
  • Rahoton ya ce, a yau Alhamis ne kotu zata zauna don yanke hukunci kan makomar Sunday Igboho
  • Lauyoyinsa, ana sa ran za su gabata a gaban kotu don bayyana kokensu da suke dashi a kan gwamnati

Wata kotu a Jamhuriyar Benin ta tsayar da ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, don fara sauraron shari’ar da ake yi wa Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa.

Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki ne ya bayyana shirin sauraren karar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, in ji PM News.

Dan awaren Yarbawan, wanda har yanzu ke hannun Brigade criminelle a Cotonou zai san makomarsa yayin sauraron karar, jaridar The Nation ta kara da cewa.

Da Dumisa: Kotu a kasar waje ta sa ranar yanke shawarin dawo da Igboho Najeriya
Dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hanyar kare Sunday Igboho

Koiki a ranar Laraba ya lura cewa sauraren karar zai baiwa lauyoyin Igboho damar gabata a can da kuma kare karar dan gwagwarmayar.

Kara karanta wannan

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

A cewarsa:

“Zan iya tabbatarwa, zai samu damar da za a saurare shi a kotun Jamhuriyar Benin, suna girmama dokokin kasa da kasa. Za zauna yau (Alhamis) da yardar Allah. Za a yi zaman ne da karfe 10 na safe a kotun Jamhuriyar Benin.
“Kotun za ta yanke hukunci kan makomar mika shi kuma za mu samu damar gabatar da kararmu musamman kan halin Igboho.
“Mun san girman abin da gwamnatin Najeriya ke kokarin yi idan suka yi kokarin ganin sun kamo Igboho amma za su gaza, da yardar Allah. Nufinsu shi ne su kama shi (Igboho), amma Allah ya yi ya kare shi.”

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

A wani labarin, an bayyana cikakkun bayanai game da yadda jami'an tsaro suka kama dan awaren Yarbawa Sunday Adeyemo (wanda aka fi sani da Igboho) ga duniya baki daya.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, Lauyan Igboho, Yomi Alliyu (SAN) ya bayyana cewa wanda yake karewa na kokarin hawa jirgin zuwa kasar Jamus tare da matarsa Bajamushiya lokacin da jami'an 'yan sanda na Interpol suka bi su tare da kwamushe su.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

Alliyu ya ce an danke shi ne a Jamhuriyar Benin, wata kasar Afirka mai makwabtaka da Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel