Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya

Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya

  • Wata kungiyar Yarbawa ta nesanta kanta da ra'ayin aware irin na Sunday Igboho mai rajin kare hakkin Yarbawa
  • Kungiyar ta ce ita tana tare da gwamnatin Najeriya, kuma ba za ta nade hannu tana kallo a lalata yankin Yarbawa ba
  • Hakazalika ta yi kira ga a ba gwamnati adin kai wajen tabbatar da an zakulo 'yan ta'adda a duk inda suke a Najeriya

Wata kungiyar Yarbawa mai suna Yoruba Appraisal Forum (YAF) ta ce ta dukufa kan hadin kai da zaman lafiya a kasar, jaridar Cable ta ruwaito.

Kungiyar ta ce ta saba da ra'ayin ballewar yankin kudu maso yamma da wasu ke fafutuka.

Ayo Animashaun, kodinetan kungiyar ta YAF na kasa, a wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce karuwar aikata laifuka a yankin kudu maso yamma na da nasaba da neman ballewar yankin.

Ya roki ‘yan Najeriya da su ba gwamnati hadin kai wajen yaki da rashin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

KARANTA WANNAN: Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

Bayan Kame Sunday Igboho, Yarbawa sun magantu kan ra'ayin ballewa daga Najeriya
Dan awaren Yarbawa, Sunday Igboho | Hoto: dailytrust.com
Asali: Instagram

Sanarwar ta ce:

"Mu kungiya ce mai bin doka da kishin kasa wacce babban burinta shi ne hadin kan dukkan 'yan Najeriya karkashin yanayin zaman lafiya da ci gaba."
“Ba za mu nade hannayenmu ba muna kallo wasu 'yan ta'adda da sunan rajin aware su gayyato ta’addanci a Kudu-maso-Yamma ba.
“Dole ne gaba daya mu himmatu domin tabbatar da zaman lafiya a yankin mu na Kudu maso Yamma da kuma kasar mu baki daya.
“Yakin da muke yi na neman zaman lafiya yaki ne da kowa yake yi da wadannan makiyan kasa kuma bai kamata a bar shi ga gwamnati ita kadai ba.

“Duk wani shiri na wargaza kasar Yarbawa ba zai yi tasiri ba kuma za mu yi biris da shi ba. Asaran rayukan marasa laifi a Najeriya ya isa haka.”

Kara karanta wannan

Duk da ba ayi wa Ibo adalci a Najeriya, ba za mu goyi bayan Biyafara ba – Dattijon Neja Delta

An kame Sunday Igboho a Jamhuriyar Benin

Bayanin kungiyar na zuwa ne a daidai lokacin da aka kama Sunday Igboho, mai rajin aware na yankin Yarbawa, a Cotonou dake Jamhuriyar Benin.

Magoya bayan Igboho sun gudanar da zanga-zanga a jihar Oyo biyo bayan tsare shi.

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

‘Yan sanda dauke da makamai sun tarwatsa magoya bayan Sunday Igboho da ke gudanar da zanga-zanga a Ibadan don nuna adawa da kamun dan awaren na Yarbawa.

An cafke Igboho ne tare da Matarsa Ropo a daren Litinin a Cotonou, Jamhuriyar Benin a kan hanyarsa ta zuwa Jamus, jaridar Punch ta tattaro.

Su biyun a yanzu haka suna tsare a Jamhuriyar Benin. Sai dai, Gwamnatin Tarayya ba ta ce komai game da kama Igboho da tsare shi a cikin kasar ta waje ba.

KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

A wani labarin, an bayyana cikakkun bayanai game da yadda jami'an tsaro suka kama dan awaren Yarbawa Sunday Adeyemo (wanda aka fi sani da Igboho) ga duniya baki daya.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, 20 ga watan Yuli, Lauyan Igboho, Yomi Alliyu (SAN) ya bayyana cewa wanda yake karewa na kokarin hawa jirgin zuwa kasar Jamus tare da matarsa Bajamushiya lokacin da jami'an 'yan sanda na Interpol suka bi su tare da kwamushe su.

Alliyu ya ce an danke shi ne a Jamhuriyar Benin, wata kasar Afirka mai makwabtaka da Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel