An kaiwa shugaban kasan rikon kwaryan Mali farmaki a filin Idi

An kaiwa shugaban kasan rikon kwaryan Mali farmaki a filin Idi

  • Wani tsagera ya kaiwa shugaban kasar Mali, Assimi Goita, farmaki a filin idin babbar sallah
  • Tuni jami'an tsaro suka cukuikuiyi mutumin da yayi kokarin sokawa shugaban kasan wuka
  • Duk da ba a tabbatar da irin raunin da Goita ya samu ba, wani jami'i yace yana cikin koshin lafiya

Bamako, Mali

An kaiwa Shugaban kasan rikon kwarya na kasar Mali, Assimi Goita, farmaki yayin sallar dinin babbar sallah, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.

Ta samu labarin ne daga ofishin shugaban kasa, inda tace harin ya faru ne a babban masallacin kasar dake Bamako.

"Tuni jami'an tsaro suka fi karfin mai kai farmaki kuma an fara biincikar lamarin," fadar shugaban kasan ta wallafa a shafinta na Twitter.

KU KARANTA: Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi

An kaiwa shugaban kasan rikon kwaryan Mali farmaki a filin Idi
An kaiwa shugaban kasan rikon kwaryan Mali farmaki a filin Idi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kano ta soke yin dukkan hawan sallah da shagulgula

Kara karanta wannan

Eid-el-Kabir: Bidiyo ya nuna Buhari yana tafiya zuwa filin Idi a Daura yayin daama'a ke taya shi murna

An yi hanzarin dauke Goita daga wurin kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na AFP yace. Sai dai ya ce ba a sani ba ko shugaban kasan ya samu rauni.

Jami'i daga fadar shugaba Goita ya magantu

Wani jami'i daga fadar shugaban kasan daga bisani ya sanar da AFP cewa Goita na cikin koshin lafiya.

Shugaban kasan ya dawo daga wani sansanin soji ne dake Kati, wajen Bamako inda aka kara jaddada tsaro, cewar jami'in.

Ministan harkokin addini, Mamadou Kone ya sanar da manema labarai cewa mutumin yayi kokarin kashe shugaban kasan da wuka amma sai aka kama shi.

Latus Toure, daraktan babban masallacin ya ce wanda ya kai farmakin ya so samun shugaban kasan amma sai ya raunata wani.

Yadda Assimi Goita ya hau mulki

An rantsar da shugaban kasan mai shekaru 37 a watan da ya gabata duk da caccakar da ya dinga fuskanta daga duniya.

A watan Augustan shekarar da ta gabata, Kanal Goita ya jagoranci juyin mulki inda ya hambarar da gwamnatin Shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita bayan watannin da aka dauka ana yi wa gwamnatin zanga-zanga sakamakon kasa shawo kan matsalar tsaro da tayi.

Kara karanta wannan

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

A karshen watan Mayu, Goita wanda yake matsayin mataimakin shugaban gwamnatin mika mulki, ya sake kwace shugabancin kasar daga shugaba bah Ndaw da firayim minista Moctar Ouane.

A wani labari na daban, wasu mazauna yankuna a jihar Zamfara a ranar Litinin sun bada labarin yadda suka ceci matukin jirgin yaki jim kadan bayan ya sauka daga kumbo bayan hatsarin jirgin yakin a ranar Lahadi.

Har yanzu dai ba a san halin da sauran wadanda ke cikin jirgin suke ba, Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi masu karfi sun sanar da Daily Trust cewa jirgin yakin ya fadi ne a wani yanki dake da kusancin kilomita 15 daga garin Dansadau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel