Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci

Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci

  • An bukaci sojojin Najeriya dake aiki da Operation Hadin Kai a yankin arewa maso gabas da su nuna kwarewarsu a kare kasar nan
  • Dakarun sojin sun samu wannan umarnin ne daga kwamandan sashin, Manjo Janar Christopher Musa a cikin kwanaki nan
  • Manjo Janar Musa ya yi wa sojojin alkwarin cewa shugabanninsu ba zasu bar su ba, ba tare da goyon baya ba wurin yaki da ta'addanci

Manjo Janar Christopher Musa, kwamandan rundunar hadin guiwa ta tsaro dake yankin arewa maso gabas ta Operation HADIN KAI (OPHK) yayi kira ga sojojin sashin da su mamaye dukkan yankunan domin yakar ta'addanci tare da dawo da zaman lafiya.

Musa ya bada wannan umarnin ne yayin ziyarar da ya kaiwa dakarun bataliya ta 68 da birged ta 5 dake filin daga na Malam Fatori da Damasak.

KU KARANTA: An kama miyagun da suka yi garkuwa da mahaifin tsohon gwamna a jihar Filato

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno

Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci
Boko Haram: An baiwa dakarun sojin Najeriya sabon umarni kan yakar ta'addanci. Hoto daga Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi

Ya je duba yanayin ayyukan dakarun da kuma hanyar gane juna da gabatar da kanshi ga dakarun da aka tura yankin.

Kamar yadda yake kunshe a wata takardar da kakakin rundunar sojin kasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, TC Musa ya karawa sojojin karfin guiwa da su kasance jajirtattu.

Ya tabbatarwa da sojojin cewa shugabannin rundunar sojin kasan ba zasu yi kasa a guiwa ba wurin baiwa mayakan goyon baya wurin yaki da ta'addanci.

Wani sashi na takardar yace: "Janar Musa yace, a matsayin garuruwan iyaka da Nijar da Najeriya suke, wurare ne da sai an bi su da dabara kuma dole ne dakarun soji su mamaye wurin.

"Ya tabbatarwa da sojojin cewa shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya tabbatar da cewa za a samar da dukkan goyon baya da kayan aiki da daakarun ke bukata wurin yakar ta'addanci."

Kara karanta wannan

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kano ta soke dukkan hawan gargajiya tare da shagulgulan babbar sallah a wannan shekarar, Daily Trust ta wallafa.

Wannan matakin na zuwa ne bayan mako daya da kwamitin fadar shugaban kasa na lura da korona ya bayyana wasu jihohi shida da suka hada da Kano a cikin jihohin da za a iya samun barkewar cutar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammadu Garba wanda ya sanar da hakan yace za a yi sallar idin babbar sallah ne a dukkan masarautu biyar da kuma masallatan dake fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel