2023: Abubakar Yar’adua ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina

2023: Abubakar Yar’adua ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina

  • Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua ya magantu a kan kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a 2023
  • Yar'adua ya ce har yanzu yana kan tuntube-tuntube da neman shawarwari daga magoya bayansa da masu ruwa da tsaki a jihar
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wakilan magoya bayansa daga dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar

Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua ya ce har yanzu yana tuntubar magoya bayansa da masu ruwa da tsaki kuma zai bayyana matsayinsa a nan gaba, gabanin zaben gwamna na 2023 a jihar Katsina.

Yar’adua ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, 19 ga wata Yuli, lokacin da ya karbi bakuncin wakilan magoya bayansa daga dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

2023: Abubakar Yar’adua ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takarar kujerar gwamnan Katsina
Abubakar Yar’adua ya ce yana kan neman shawarwari kafin ya yanke hukuncin neman takarar kujerar gwamnan Hoto: Senator Yar'adua Reality
Asali: Facebook

Ya ce:

“Ina ta samu kiraye-kiraye daga dukkan sassan jihar, suna tambayata game da burin zama na gwamna kuma ina fada wa mutanena cewa har yanzu muna ci gaba da tuntubar shugabannin jam’iyyarmu a kan wannan batun kuma zan sanar da matsayina idan lokaci ya yi."

Kara karanta wannan

Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

Ya ci gaba da cewa:

“Ina da yakinin cewa ba ‘yan siyasa kadai ba har ma da dukkan ‘yan jihar za su yi maraba da wannan tunanin wanda ba za a bar wani rukuni ya karkatar daa jam’iyya ba ko kuma ya tursasa dan takara ba. Wannan shi ne abin da ake fata ga shugaba nagari wanda zai saurari dukkan bangarori kuma ya yi adalci ga duk wanda abin ya shafa.”

Ya yi gargadin cewa idan har wata kungiya ko wani bangare na ‘yan siyasa a jihar suka yi kokarin rusa kyakyawan tsari da gwamnan ya yi, jam’iyyar za ta gamu da rarrabuwar kai a jihar.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin wanke bandaki a Abuja na tsawon kwanaki 60 kan yunkurin damfara

A wani labari na daban, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jiharsa ta Katsina ranar Alhamis, kuma ana tsammanin zai ƙaddamar da aikin ruwa na Zobe Dam da ya laƙume biliyoyin kuɗi da kuma hanyar Dutsinma-Tsaskiya mai kilomita 50, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da mai taimakawa gwamnan Katsina kan yaɗa labarai, Abdu Labaran Malumfashi, ya fitar.

Gwamnatin Buhari ta ƙarisa aikin ruwa na Zobe Dam shekara 40 bayan fara shi, yayin da gwamnatin Katsina ta aiwatar da aikin hanyar Dutsinma-Tsaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel