Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci yan Najeriya da su ƙara hakuri da gwamnatinsa
  • Shugaban ya taya ɗaukanin yan Najeriya murnar zagayowar babbar sallah (eid-el-kabir)
  • Buhari yace addinin musulunci bai koyar da tsananta farashin abinci da na dabbobi ba don samun riba

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga yan Najeriya da su ƙara hakuri da gwamnatinsa yayin da take ƙoƙarin warware musu matsalolin rayuwa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

Yayin da yake taya al'ummar ƙasar murnar babbar sallah, Buhari ya alaƙanta ƙalubalen da Najeriya ke fama da shi da ɓarkewar annobar COVID19, matsalar tsaro, da kuma ambaliyar ruwa dake hana samar da kayan abinci.

Shugaban ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ginawa da inganta ƙasar nan, inda zaman lafiya da kwanciyar hankali zai samu gindin zama, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Masarautar Zazzau Ta Soke Bikin Hawan Salla Saboda Cutar Korona

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

A saƙon shugaban yace:

"Banda matsalar da ake samu wajen noman shinkafa saboda ambaliyar ruwa, mutanen tsakiya suna amfani da damar shinkafar mu ta gida da muke samar wa suna cutar da yan Najeriya.

"Ba dan komai ba sai don su rushe kudirin mu na taimakawa wajen samar da abinci a cikin gida a farashi mai rahusa."

"A matsayina na zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da al'umma suka damƙa amanar su gare mu, ina tabbatar muku cewa muna iyakar ƙoƙarin mu wajen ganin an sauƙaƙa wa yan ƙasa, wanda ya haɗa da samar da takin noma cikin farashi mai sauƙi ga manoman mu."

Matsalar tsaro

Shugaba Buhari ya ƙara da tabbatarwa yan Najeriya cewa matsalar tsaron Najeriya mai ƙarewa ce, inda yace:

"Wannan matsalar tsaron da muke ciki ta shafi ɓangaren noma ta kowane fanni domin manoma sun rasa damar zuwa gonakinsu cikin kwanciyar hankali."

"Ina amfani da wannan damar in ƙara tabbatar wa yan Najeriya cewa muna ɗaukar duk wani mataki domin magance ƙalubalen tsaro."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

"Jiragen yaƙi da sauran makaman sojoji sun fara isowa gare mu, kuma makaman zasu ƙara wa jami'an tsaron mu karfin guiwa wajen tunkarar yan bindiga da yan ta'adda."

KARANTA ANAN: Cutar COVID19: NAFDAC Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ba Ta Amince da Magungunan Gargajiya Ba

Shugaba Buhari ya taya musulmai murna

Yayin da yake jawabi kan muhimmancin sallah babba (Eid-el-kabir), Buhari ya roƙi al'ummar musulmai "Su nuna kyawawan ɗabi'un addinin musulunci ta hanyar zama abin misali a ayyukansu."

Buhari yace: "Yin amfani da shagulgulan sallah wajen cutar da yan ƙasa ta hanyar ƙara farashin abinci da ragon layya, ba koyarwar addinin musulunci bace."

"A matsayin mu na masu imani, bai kamata mu nemi riba mai yawa ba wacce zata jefa rayuwar wasu cikin matsanancin hali."

A wani labarin kuma Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Ibrahim Gambari, ya roƙi yan Najeriya su baiwa gwamnatin Buhari goyon baya.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Nasarar Shugaba Buhari Nasarar Ku Ce, COS Ga Yan Najeriya

COS Gambari ya yi wannan kira ne yayin da ya isa mahaifarsa Ilorinɓa karon farko tun bayan naɗinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel