An Kama Ƴan Ƙasar Isra’ila 3 Da Ke Da Alaƙa Da Ƙungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu

An Kama Ƴan Ƙasar Isra’ila 3 Da Ke Da Alaƙa Da Ƙungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu

  • Jami'an DSS a Nigeria sun kama wasu yan Isra'ila uku da suka tafi jihar Anambra domin hada fim
  • An kama mutane ukun ne kan zarginsu da alaka da haramtaciyyar kungiyar ta IPOB mai son ballewa daga Nigeria
  • A bangarensu, iyalan wadanda aka kama sun ce yan uwansu sun kai wa mutanen garin da suka ziyarta ne kyautuka amma basu goyon bayan IPOB

Hukumar yan sandan farin kaya ta DSS ta kama wasu mutane uku yan asalin kasr Isra'ila masu shirya fim kan zarginsu da alaka da kungiyar 'yan aware masu son kafa kasar Biafra wato IPOB, Daily Trust ta ruwaito.

Yan kasar na Isra'ila, Rudy Rochman, dan gwagwarmaya na Isra'ila; Noam Leibman, mai hada fim da David Benaym, Dan jarida dan kasar Faransa-Isra'ila, an kama su ne a ranar 9 ga watan Yuli lokacin da suka ziyarci kauyen Ogidi da ke karamar hukumar Idemili ta jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

An Kama Ƴan Ƙasar Isra’ila 3 Da Ke Da Alaƙa Da Ƙungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu
An Kama Ƴan Ƙasar Isra’ila 3 Kan Zargin Alaƙa Da Ƙungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ku Bar Gari Ko Mu Aurar Da Ku: Ciyaman Ya Bawa Karuwai Wa’adin Kwana 30 a Jigawa

An ce yan kasar wajen sun baro fili n tashin jirage na Ben Gurion a Isra'ila ne a ranar 5 ga watan Yuli sannan suka iso Nigeria a ranar 6 ga watan Yuli domin nadar wani fim mai suna 'We Were Never Lost'.

The Cable ta ruwaito cewa fim din zai mayar da hankali ne kan wasu garuruwa a kasashen Afrika kamar Kenya, Madagascar, Uganda da Nigeria da ake ganin akwai masu bin addinin Yahudanci.

A cewar jaridar Times of Isreal, gwamnatin Nigeria bata tuhume wadanda aka kama din da wani laifi ba kuma ba su da lauyoyi da za su kare su.

Jaridar ta ce an kama masu hada fim din ne kan zargin sun zo su gana da masu son kafa kasar Biafra.

Iyalan yan Isra'ilan uku da aka kama su ce wasu mutane a Nigeria domin dalilan siyasa suna yi wa kyautar Attaura da suka bawa mutanen garin a matsayin goyon bayansu na ballewa daga Nigeria.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

KU KARANTA: Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

A cikin sanarwar, yan uwan masu hada fim din da aka kama sun ce kyautan da yan uwansu suka bawa mutanen na Nigeria baya nufin suna goyon bayan abubuwan da IPOB ke yi.

Sanarwar ta ce:

"Masu hada fim din sunyi tunanin zai dace su bawa yan garin da za su kai ziyara kyaututuka a matsayin karamci, amma wasu masu manufofin siyasa sunyi amfani da hotunan bada kyautan da wata manufa daban."

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel