Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

  • Shugaban hafsan sojojin Najeriya ya tabbatar wa 'yan Najeriya kudurinsa na inganta tsaron kasa
  • Ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa, Najeriya ta dawo daidai kamar yadda take da
  • Ya kuma ce ba zai bari ba, dole sai ya hukunta ganganci da sakaci a wajen aiki don tabbatar da aiki tukuru

Babban hafsan sojoji, Janar Faruk Yahaya, ya baiwa 'yan Najeriya tabbacin cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da mai da hankali wajen magance dumbin matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Yahaya ya bayar da tabbacin ne a sakonsa na fatan alheri ga hafsoshi, sojoji da danginsu kan bikin Babbar Sallah na 2021, ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, a Abuja.

Ya ce bikin na Babbar Sallah ya nuna kyawawan dabi'u na biyayya, mika kai da sadaukarwa wadanda su ne manyan kwarewa ta aikin sojoji, Punch ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Shugaban hafsan soji ya bukaci 'yan Najeriya su kwantar da hankali, ana aikin kare kasa
Laftanal-Janar Farukh Yahaya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Don haka bikin Idi ya ba mu wata dama ta musamman a gare mu don yin tunani da rubanya kokarinmu wajen cika matsayinmu na tsarin mulki na fatattakar abokan adawarmu da kuma kare martabar Najeriya.
“Babu shakka, Kasar na fuskantar dimbin kalubalen tsaro, Sojojin Najeriya zuwa yanzu sun kai yadda ake tsammani kuma za su ci gaba da kasancewa da himma wajen tunkarar wadannan matsalolin.
“Don haka, ina so musamman in yaba da irin sadaukarwar da sojojinmu suka yi a Operation Hadin Kai, Hadarin Daji, Thunder Strike, Whirl Stroke da duk sauran ayyukan da Sojojin ke yi a ciki da wajen kasar.
“Bari na yi amfani da wannan damar don sake jinjina ta musamman ga abokan aikinmu wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen kare kasarmu. Fatan su huta a makwancinsu cikin kwanciyar hankali."

Zan cika alkawuran aiki

Janar Faruk Yahaya ya ce zai cika alkawarin da ya dauka na inganta cancanta, jarumta, kwarewa, kwazo, sadaukar da kai, bikin kwarewa da girmama “gwarazanmu”.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Ya kuma ce zai ba da sakamako mai kyau da nasarori, ya kara da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta rashin da'a, rashin kulawa, sakaci da duk wasu abubuwa marasa kyau, Premium Times ta tattaro.

KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan hukuncin harbe 'yan bindiga a Najeriya

A wani labarin, Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce harsasai da sauran karfin makamai su kadai ba za su iya dakatar da fashi da makami, bindiganci da sauran nau'ikan aikata laifuka a kasar ba.

Ya fadi haka ne a ranar Lahadi a Abuja yayin bikin cikar shekaru 50 na tsohon Corps Marshal na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Osita Chidoka.

A cewarsa, magance ta'addanci da aikata laifuka yana bukatar manyan shirye-shirye masu inganci na gwamnati, fasaha da sauran dabaru, Reuben Abati ya tattaro.

Kara karanta wannan

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

Asali: Legit.ng

Online view pixel