Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

  • Kwamitin yaki da cutar Korona a Najeriya ya shawarci wasu jihohi su dage bukukuwan sallah
  • Wannan ya biyo bayan sake barkewar cutar Korona a Najeriya, wacce ta kara kamari a cewar kwamitin
  • Hakazalika, kwamitin ya jero jihohin da cutar ta fi saurin yaduwa tare da bayyana gargadi gabanin sallah

Kwamatin yaki da cutar korona na Gwamnatin Tarayyar Najeriya ya saka jihohi shida da kuma Abuja cikin mafiya hadarin yaduwar cutar sannan ya shawarce su da su soke bukukuwan Babbar Sallah, BBC Hausa ta ruwaito.

Shugaban kwamatin Presidential Steering Committee (PSC) kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Asabar.

Ya zayyana jihohin kamar haka: Legas, Kano, Kaduna, Oyo, Rivers, Filato da Abuja. Mista Mustapha ya ce shi kansa fitar da jerin sunayen mataki ne na yaki da yaduwar cutar.

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Kara karanta wannan

Cutar kwalara ta barke a Abuja, mutane 604 sun kamu, 54 sun riga mu gidan gaskiya

Bukukuwan Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano ta soke hawan sallah
Hawan sallah a jihar Kano | Hoto: ytimg.com
Asali: UGC

Kamar yadda yazo a Daily Trust, Mustapha ya ce:

"Wadannan matakan na da muhimmanci sosai yayin da muke ganin karuwar masu kamuwa da cutar a Najeriya."
"Kwamatin PSC na taya Musulmai murnar Eid-el-Kabir (Idin Babbar Sallah). Sai dai yana shawartar gwamnatocin jiha da shugabannin addini da su san cewa akwai yiwuwar yaDuwar cutar duk sanda aka tara dubban jama'a."

Saboda haka ne kwamatin ya shawarci jihohin da su soke Hawan Sallah sannan kuma a yi Sallar Idi a masallatan Juma'a.

Matakin ya biyo bayan bullar nau'in cutar mai suna Delta a jihohin kasar da kuma karuwar masu kamuwa da ita da wadanda ake kwantarwa a asibiti.

Masarautar Katsina: Abin da ya sa mu ka dakatar da bikin hawan Sallar Azumi

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabiru Usman CFR, ya bada sanarwar ba za a gudanar da bukukuwan hawan sallah a shekarar bana ba.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Abdulmumin Kabiru Usman ya sanar da daukacin mutanen Katsina cewa matsalar sace-sace da kashe-kashen da ake yi ya sa aka dauki wannan matakin.

Sarkin ya bayyana cewa shawarwarin da ya samu daga gwamnati, jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya suka sa aka yi watsi da shagulgulan karamar sallah.

KARANTA WANNAN: Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno

Babbar Sallah: Dillalan raguna sun fara kokawa, sun ce ga raguna birjik babu mai saye

A wani labarin, 'Yan kwanaki kadan kafin gudanar da bikin Babbar Sallah, dillalan ragunan layya sun fara koka rashin ciniki yadda ya kamata a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), wanda ya ziyarci wasu kasuwannin raguna a sassa daban-daban na llorin a ranar Alhamis ya ruwaito cewa dillalan ragunan da dama sun koka da karancin ciniki.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnati Ta Kame Sheikh Abduljabbar, Ta Turashi Magarkama Ya Yi Sallah

Akwai adadi masu yawa na raguna a dukkan kasuwannin da aka ziyarta, inda dillalan ke jiran masu siye da jiran tsammani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel