Abduljabbar: Wasu fitattun Malaman addini da suka shiga hannun Jami'an tsaro a gida da waje

Abduljabbar: Wasu fitattun Malaman addini da suka shiga hannun Jami'an tsaro a gida da waje

A tarihin rayuwa, malamai sun saba samun sabani da hukumomi da gwamnati

Wannan ya sa malaman addin saboda wasu dalilai su ka samu kansu a garkame

Wasu malaman kuma su kan amsa tambayoyi a kan wasu zargi da ake yi masu

Rikicin Malamai da Jami'an tsaro a tarihi

Daga cikin malaman addinin da suka shiga wannan rikici a tarihi akwai Muhammad Mai tatsine da Bala Qalarawy da irinsu Sheikh Isyaka Rabiu a shekarun baya.

Legit.ng Hausa ta kawo jerin malaman Najeriya da aka taba daure wa a gidajen yari, aka tsare a hannun jami’an tsaro, ko kuma aka yi ram da su a kasashen ketare.

1. Abduljabbar Nasiru Kabara

Malamin da ya samu kansa a wannan hali kwanan nan shi ne Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da laifin zagin Manzon Allah SAW, malamai da neman kawo hayaniya.

2. Ibrahim Zakzaky

Tun karshen 2015, jagoran kungiyar IMN ta mabiya shi’a, Ibrahim Zakzaky ya ke tsare bayan takaddama da sojoji. A baya Zakzaky ya yi ta samun matsala da gwamnatoci da hukuma.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

3. Bello Yabo

A 2020 ne jami’an tsaro suka kama babban malamin nan na Sokoto, Sheikh Bello Yabo kan sukar hana yin sallar idi saboda COVID-19. Kafin nan, gwamnati ta saba kama shi, har ya sha dauri.

KU KARANTA: Gwamnati ta kama Sheikh Abduljabbar Kabara, zai yi zaman kaso

4. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya shiga hannun jami’an kasar Saudi a 2010. An daure Malamin na tsawon watanni bisa zarginsa da ake yi da alaka da wani ‘dan ta’adda, Faruk Umar Mutallab.

5. Mohammed Yusuf

Mohammad Yusuf ne wanda ya kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya. A 2009, jami’an sojoji suka cafke shi, aka mika shi hannun ‘yan sanda, inda ake zargin su kuma suka hallaka shi.

6. Mohammed Nazifi Yunus

A shekarar 2013 jami’an tsaro suka kama Dr. Mohammed Nazifi Yunus Jos. An zargi malamin mai koyar wa a jami’ar jihar Kogi da cewa ya na cikin ‘yan Boko Haram masu yakar ilmin boko.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnati Ta Kame Sheikh Abduljabbar, Ta Turashi Magarkama Ya Yi Sallah

7. Ibrahim Jalo Jalingo

Sai a 2016 gwamnan Taraba, Darius Ishaku ya dakatar da wasu malaman jami’ar jiha, daga ciki har da Dr. Jalo Jalingo. Jalingo na cikin malaman da ke samun sabani da gwamnatin Taraba.

8. Dr. Ahmad Ibrahim

An taba kai karar Sheikh Ahmad Ibrahim BUK gaban ‘yan sanda a jihar Kano. Wadanda suka kai dattijon malamin wajen hukuma sun fusata ne bayan karatun da ya yi a kan Darikar Tijjaniyah.

KU KARANTA: Kungiya ta ja-kunnen Osinbajo kan kawo tsare-tsaren nakasa Arewa

Malaman addini
Malaman da aka taba kama wa Hoto: hausa.legit.ng
Asali: Original

9. Muhammad Aminu Usman

A Mayun 2019 ne jami’an tsaro suka kama Malam Muhammad Aminu Usman wanda aka fi sani da ‘Abu Ammar’ bayan wata huduba mai zafi da ya yi a kan lamarin tsaro a jihar Katsina.

10. Idris Abdulaziz

Wani malami a wannan jerin shi ne Ustaz Idris Abdulaziz. Jami’an DSS na reshen jihar Bauchi sun zauna da malamin, kafin ayi gaba da shi zuwa ofishinsu da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Khalifa Sanusi II ya jinjinawa Malaman da suka kalubalanci Abduljabbar, ya yi kira ga al'umma

11. Sani Yahaya Jingir

Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya fada hannun jami’an DSS bayan ya fito ya na maganganu a kan annobar COVID-19. Bayan ya fito, shehin malamin ya canza matsayarsa.

12. Muhammad Auwal Adam

Marigayi Muhammad Auwal Adam wanda aka fi sani da Albanin Zariya, shi ne na karshe a jerin. ‘Yan sanda sun taba kama malamin bisa wasu zargi, a karshe ya je kotu, ya samu nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel