Ortom ga Buhari: Ka daina munafunci; idan Katsina ta samu N6.25b don kiwon zamani, a ba Benue N100bn

Ortom ga Buhari: Ka daina munafunci; idan Katsina ta samu N6.25b don kiwon zamani, a ba Benue N100bn

  • Gwamnan Jihar Benuwai ya soki lamirin Gwamnatin Tarayya kan yadda ya ce tana nuna fifiko tsakanin jihohin kasar
  • Ya ce munafurci da yaudara ce a bai wa Jihar Katsina N6.5b domin kiwon zamani yayin da aka bar jiharsa
  • Ya yi ikirarin jiharsa ta dade da fara dabbaka kiwon zamani amma ba a ba ta ko sisi ba

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya ce kololuwar yaudara da munafurci ne ya sa Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira biliyan 6.25 don kiwon zamani a Jihar Katsina har ta riga ta saki Naira biliyan 5, yayin da ita gwamnatin ke neman dawo da burtalolin shanu da zimmar karfafa kiwo a fili a wasu jihohin na tarayya.

Gwamna Ortom, wanda ya fadi hakan a filin jirgin saman Makurdi, yana mayar da martani ne ga bayanan da Gwamna Bello Masari ya yi, yayin kaddamar da aikin Madatsar Ruwa ta Zobe a Dutsinma da ke Jihar Katsina, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki

Zaku tuna cewa Masari yace shugaban Kasa ya amince da N6.25b domin aikin habaka kiwon zamani a Jihar Katsina, daga cikin kudaden, N5b na cikin asusun gwamnatin jihar.

Gwamna Ortom ya kafe kan cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta nemi gafarar sa tare da bada irin wannan karimcin ga Jihar Benuwai ta hanyar tura N100b ga jihar domin kafa wuraren kiwon zamani a jihar.

Ka daina munafunci; idan Katsina ta samu N6.25b don kiwon zamani, a ba Benue N100bn, Ortom ga sghugaban Buhari
Ortom ga Buhari: Ka daina munafunci; idan Katsina ta samu N6.25b don kiwon zamani, a ba Benue N100bn Hoto: Presidency

Ya ce:

“Don haka, Maigirma Shugaban Kasa ya amince da N6.5b domin kiwon zamani a Jihar Katsina. Wannan wane irin munafurci ne? Shin muna da kasa mai ma’ana kuwa?
“Idan Shugaban Kasa zai ce Babban Lauyan Tarayya ya tabbatar da sake tashin wadanda suka keta haddin burtalolin shanu da wuraren kiwo domin dawo da yin kiwon sake duk da karuwar da jama’a suka yi daga kasa da miliyan 40 a shekarar 1950 zuwa sama da mutum miliyan 200 a yau.

Kara karanta wannan

Kano Za Ta Iya Gogayya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari

“Kuma wannan Shugaban yana karfafa gwiwar kiwo a Jihar Katsina inda ya fito, wannan tabbas abin dariya ne da munafurci da yaudara.
“Don haka idan Shugaban Kasar ya amince da N6.5b ga Jihar Katsina, to lallai ne gwamnatin ta amince da ware N100b ga Jihar Benuwai tare da neman afuwa a gare ni.

Gwamna Ortom ya kara da cewa ba daidai ba ne ga Gwamnatin Tarayya ta amince da kudi don kiwo a cikin wata jiha ta bar wasu jihohin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel