Yan ta'addan IPOB na shirin kai hari gidan yarin Kuje don kubutar da Nnamdi Kanu

Yan ta'addan IPOB na shirin kai hari gidan yarin Kuje don kubutar da Nnamdi Kanu

  • An bankado dalilin da ya Nnamdi Kanu ke son a mayar da gidan yari
  • Yan IPOB sun shahara da kai hari ofisoshin yan sanda da gidan yari
  • A baya sun kubutar da daruruwan mutane a gidan yarin Owerri

Mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB masu rajin kafa kasar Biyafara na shirin kai hari gidan yarin dake karamar hukumar Kuje, birnin tarayya Abuja.

Majiyoyi daga hukumomin tsaro sun bayyanawa PRNigeria cewa mambobin kungiyar na cire kai harin don kubutar da shugabansu, Nnamdi Kanu, da ke tsare a wajen.

Zaku tuna cewa hukumar DSS na tsare da Nnamdi Kanu tun lokacin da aka damkoshi daga kasar Kenya.

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Kanu ya bukaci babbar kotun tarayya cewa a ajiyeshi a gidan yarin Kuje saboda yana shan bakar wahala hannun hukumar DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu

A bukatar da ya gabatarwa kotu, Ifeanyi Ejiofor, lauyan Kanu ya ce ana galazawa wanda ya ke karewa azaba ta kwakwalwa da wasa da hankali a hannun DSS.

Yan ta'addan IPOB na shirin kai hari gidan yarin Kuje don kubutar da Nnamdi Kanu
Yan ta'addan IPOB na shirin kai hari gidan yarin Kuje don kubutar da Nnamdi Kanu

Yan ta'addan IPOB na shirin kai hari gidan yari

Amma wani babban jami'in tsaro ya bayyana PRNigeria cewa yan IPOB/ESN na shirin kai hari gidan yarin Kuje muddin aka mayar da Nnamdi Kanu wajen.

Yace:

"Mun gano wani shirin hari da ake son kaiwa gidan yarin Kuje. Wannan shi yasa Nnamdi Kanu ya bukaci a mayar da shi gidan yarn daga wajen DSS da ake tsare."

A cewar majiyar, yan IPOB shirya suke su kubutar da Kani ko ta 'kaka.

Ya kara da cewa sun bankado yadda mabiyansa ke yiwa jami'an tsaro da ma'aikatan kotu barazana don kawai a mayar da shi Kuje saboda su kai hari kamar yadda suka kaiwa ofishohin yan sanda da gidajen yari a kudu.

Kara karanta wannan

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Asali: Legit.ng

Online view pixel