Najeriya ce ta 98 a jerin kasashe 107 da ke fama da yunwa a duniya

Najeriya ce ta 98 a jerin kasashe 107 da ke fama da yunwa a duniya

  • Matsalar karancin abinci a kasar ta faru ne sakamakon rashin tsaro daga ‘yan ta’adda
  • Rahoton bincike ya nuna tsauraran manufofin gwamnati da wasu abubuwa na daban sun taimaka wajen hauhawar farashin abinci a Najeriya
  • Wadansu iyalai da dama sun ce yanzu suna cin abinci sau daya kadai a rana

Najeriya na fuskantar mawuyacin hali na yunwa yayin da take kasa ta 98 cikin kasashe 107 da suke fama da yunwa a rahoton Yunwar Duniya na shekarar 2020.

Har ila yau, kasar na da yawan mutanen da ba sa samun isasshen abinci a al’ummar da ke karuwa da kashi 7.6 a shekarar 2012 zuwa kashi 12.6 a shekarar 2020.

A cewar wani kamfanin tuntuba da ya mayar da hankali kan binciken kasashen Afirka, a rahotonsa ya ce matsalar abinci a kasar ya faru ne sakamakon rashin tsaro daga ‘yan ta’addan Boko Haram da ’yan bindiga da na makiyaya masu kashe mutane wadanda suka tilasta wa manoma barin gonakinsu.

Kara karanta wannan

Daga yanzu an amince shaguna su kasance a bude a lokutan sallah a Saudiyya

Sauran dalilan a cewar kamfanin, sune rashin wuraren adanawa yadda ya kamata da farashin maras tabbas da sauyin yanayi da hauhawar farashin makamashi da kayan aiki da tsauraran manufofin gwamnati da masifu na annobar Corona da rage darajar kudin kasar.

Najeriya ce ta 98 a jerin kasashe 107 da ke fama da yunwa a duniya
Najeriya ce ta 98 a jerin kasashe 107 da ke fama da yunwa a duniya
Asali: Original

A cewar rahoton Ofishin kididdiga na Najeriya (NBS) kamar yadda kamfanin ya wallafa, hauhawar abinci ya karu da kashi 48.94% (daga kashi 15.04% zuwa 22.95%).

Kamfanin binciken ya tattara bayanansa daga manyan kasuwannin abinci a duk fadin kasar kuma ya lura da yadda mutane suke kokawa da mummunan hauhawar farashin abinci wanda ya sauya yanayin rayuwarsu ta yau da kullum.

Farashin kayan abincin yau da kullum da ’yan Najeriya suka fi ci, da suka hada da shinkafa da wake da kwai da garri da plantain da doya da naman shanu da manja da kifi da barkono da tumatir da albasa da burodi da man gyada duk sun yi tashin gwauron zabi.

Kara karanta wannan

Dagacin kauye ya kai kuka game da harin da Dorina ke kaiwa kaiwa mutane a Gombe

Mafi yawan wadanda aka zanta da su a cikin masu karamin karfi sun ce yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana; sai dai su ci sau daya inda suke lallabawa da kayan kwalam da makulashe.

Misis Christiana, matar aure ce kuma 'yar kasuwa a Legas ta bayyana cewa ta koma cin abinci sau biyu a kullum, saboda alawus-alawus da take karba ba zai iya ciyar da iyalinta abinci sau uku a wuni ba.

Farashin wake da gari a kasuwar Sango-Ota ya tashi da kashi 97.9%, wanda kusan ya ninka cikin wannan lokacin da ake nazarta. Wake ya tashi daga N1,457 zuwa N2,883, gari ya kara farashi daga N869 zuwa N1,856 a kowace roba fentir guda. A cewarta, karin farashin wadannan kayan abinci guda biyu sun kasance mafi girma a cikin shekara guda da ta gabata.

Ziyara zuwa kasuwanni daban-daban ya nuna cewa a duk kasuwannin ban da kasuwannin Onitsha da Fatakwal da Calabar kudin girka tukunyar shinkafar Jollof ya yi tashin gwauron zabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel