Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari

Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari

  • Iyalan shugaban kasa Buhari sun kai lefen Zarah Bayero masarautar Kano ta dabo
  • Kamar yadda aka gano, a cikin lefen akwai akwatuna 3 na zinari da lu'u-lu'u
  • Har ila yau, an samu wasu akwatuna 2 dankare da tsabar kudi daga iyalan Buhari

Masarautar Kano

Labarai da dumi dake zuwa ma Legit.ng shine na kai gagarumin Lefen auren Yusuf Buhari, da namiji daya tilo ga shugaban kasa Buhari da aka yi masarautar Kano.

Neman aure

Tuni dai Legit.ng ta ruwaito yadda aka je neman auren Gimbiya Zarah Bayero karkashin shugabancin gwamna Badaru na jihar Jigawa inda tawagar ta cika da wasu gwamnoni, ministoci da kuma kusoshin gwamnati.

KU KARANTA: Zamfara: Luguden bama-baman NAF ya aika mata da 'ya'yanta 4 barzahu a Sububu

Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari
Daular duniya: Bidiyoyin lefen alfarma na Zarah Bayero daga Iyalin Shugaba Buhari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama

An gano cewa bayan babbar sallah Yusuf Buhari zai angwance da tsuleliyar Gimbiya, Zarah Bayero, diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Bayero.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

An kai lefe

Tuni dai shirye-shirye suka kankama tunda a ranar Alhamis iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari suka dira birnin dabo dauke da lefen alfarma.

Kamar yadda wani shafi mai suna @arewafamilyweddings ya wallafa a Instagram, ya tabbatar da cewa an mika lefen masarautar Kano.

Lefen ya kunshi akwatuna uku dankare da zinarai da lu'u-lu'u, yayin da akwatuna biyu ke cike da tsabar kudi daga iyalan shugaban kasan.

Kamar yadda wallafar ta zo, "Muna taya Gimbiyarmu murna. Kudi sun yi. Duba akwatuna 3 cike da zinarai da lu'u-lu'u da kuma akwatuna biyu dankare da tsabar kudi daga iyalan shugaban kasa."

Ba wannan shafin kadai ya wallafa labarin lefen ba, shafin gidan sirikan Zarah Buhari, mai amfani da suna @keepingupwiththeindimis.

Shafin ya taya Yusuf Buhari murna inda ya kara jaddada cewa an kai lefen masarautar Kano.

A wani labari na daban, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rangwantawa talakawa. Basaraken yayi wannan kiran bayan karbar bakuncin shugaban kasan a fadarsa a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Ya yi kira ga shugaban kasan da ya inganta tsaro tare da shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

"Muna godiya ga shugaban kasa kan wannan ziyarar kuma hakan zai kara dankon alakarsa da gidan sarauta. Gidansa ne dama can. Ba za mu iya fadin sau nawa ya zo gidan ba ballantana a zamanin marigayin Sarki, a yayin shagali da babu," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel