Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno

Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno

  • Wani turmutsutsin karɓar abinci a sansanin yan gudun hijira dake Monguno ya hallaka mata masu juna biyu
  • Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mata 10 ne suka mutu, waɗanda mafi yawansu masu juna biyu ne ko shayarwa
  • Ƙungiyar agaji ta Red Cross ce take raba wa yan gudun hijiran abinci yayin da lamarin ya faru

Aƙalla mata 10 waɗanda mafi yawan su masu juna biyu ko masu shayarwa ne suka rasa rayukansu yayin ƙoƙarin karbar abinci a Monguno, jihar Borno, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Wani Gwamnan Arewa Ya Bada Umarnin Biyan Ma'aikatan Jiharsa Albashi Kafin Sallah

Rahotanni sun bayyana cewa matan sun rasa rayukansu ne a turmutsutsin karɓar abincin da zasu ci a sansanin yan gudun hijira.

Wannan lamarin ya faru ne yayin da wata ƙungiya ta kai musu agajin abinci a sansanin yan gudun hijira dake Mungonu.

Wajen raba abinci
Rububin Karbar Abinci Ya Hallaka Mata Masu Juna Biyu da Dama a Borno Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Ƙungiyar agaji ta Red Cross, wanda ta raba abincin, ta bayyana rashin jik daɗin ta da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu

Ƙungiyar ta yi gaggawar nemo kayan agaji domin taimakawa waɗanda suka ji raunuka yayin wannan turmushin.

An harba hayaƙi mai sa hawaye

Wata majiya ta bayyana cewa jami'an yan sanda ne suka harba hayaƙi mai sa ƙwalla domin tarwatsa taron.

"Mutane sun firgita, inda suka fara guje-guje bayan an harba hayaƙi mai sa ƙwalla domin tarwatsa taron." inji majiyar.

KARANTA ANAN: Layin Dogo: Gwamnatin Tarayya Zata Dauki Ma'aikata 20,000 Aiki, Minista

Legit.ng hausa ta gano cewa aƙwai aƙalla yan gudun hijira 100,000 a sansanin dake Monguno, kuma dukkan su rikicin Boko Haram ne ya raba su da gidajensu.

A wani labarin kuma Rundunar Sojin Sama Ta Faɗi Ranar da Jiragen Yaki 'Super Tukano' Guda 6 Zasu Iso Daga Amurka

Rundunar sojin sama NAF ta tabbatar da cewa jiragen yaƙin super tucano guda shida sun baro Amurka.

A wani jawabi da kakakin NAF ya fitar, yace jiragen zasu biyo ta wasu ƙasashe biyar kafin isowar su.

Kara karanta wannan

Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka Ta Yi Wuf da Dan Najeriya, Ta Canza Suna

Asali: Legit.ng

Online view pixel