An Kama Mai Gadi Da Ya Haɗa Baki Da Wasu Domin Sace Manajan Bankin Da Ya Ke Aiki

An Kama Mai Gadi Da Ya Haɗa Baki Da Wasu Domin Sace Manajan Bankin Da Ya Ke Aiki

  • An kama wasu mutane biyu da ake zargi da shirin sace manajan banki a Ekpoma jihar Edo
  • Felix Alika, mai gadi a bankin ya tuntubi Suleiman Basiru da Akhere don su taimaka masa
  • Amma kafin ranar da za a aikata laifin, Akhere ya sauya ra'ayinsa ya tafi ya kaiwa yan sanda rahoto

Yan sanda a jihar Edo sun kama mutane biyu da suka shirya yadda za a sace manajan banki bayan daya daga cikin wadanda aka hada baki da shi domin aikata laifin ya tuba ya kaiwa yan sanda rahoto

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama Felix Alika da Suleiman Basiru domin shirya sace Mr Raphael Ibodeme, manajan daya daga cikin bankunan zamani a Nigeria mai reshe a Ekpoma.

An Kama Mai Gadi Da Ya Haɗa Baki Da Wasu Domin Sace Manajan Bankin Da Ya Ke Aiki
Yan sandan Nigeria. Hoto: The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Alika, wanda mai gadi ne a bankin ya shirya yadda za a sace manajan da wani Bashiru da Akhere kamar yadda PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Kwanaki kadan kafin a aikata laifin, Akhere ya tuba sannan ya kai wa yan sanda rahoto, hakan yasa nan take aka kama sauran wadanda suka shirya abin tare.

Alika ya shaidawa yan sanda cewa manajan bankin mai laifi ne kuma shine ke shirya fashin bankuna da ake yi a yankin.

An gano cewa binciken na yan sanda ya nuna cewa Alika ya dade yana rikici da manajan bankin saboda rashin bin umurninsa hakan yasa ya dauki wasu matakai a kansa.

KU KARANTA: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Rikicin da ke tsakanin Alika da manajan ya sa ya tuntubi Akhere, wanda shi kuma zai dauki hayan wasu bata garin da za su sace manajan.

A bangarensa, mai magana da yawun yan sandan jihar Edo, SP Kontongs Bello ya ce rahoto daga sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ya nuna mai gadin, Alika, ya yi wa Ibodeme sharri ne.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Ya bada tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel