Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

Dalla-dalla: Bayanin yadda ake cike fom na neman ayyukan gwamnati 3 da ake dauka yanzu

Akalla ma'aikatun gwamnatin tarayya uku ne ke shirin daukar ma'aikata a wannan shekarar, wadanda suka hada hukumar sojin kasa ta Najeriya, sojin sama da hukumar kula da hadurran kan hanya ta kasa wato FRSC.

Don tabbatar da 'yan Najeriya masu sha'awar neman ayyukan ba su fada hannun 'yan damfara ba, wannan rubutu ya bayyana hanyoyin da ake wajen neman aikin cikin sauki.

KARANTA WANNAN: Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

Dalla-dalla: Ayyukan gwamnati da ake cikawa a yanzu, da yadda ake cikawa
Hukumomin tsaro | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Sojin kasa na Najeriya

Hukumar sojin Najeriya na karbar takardun neman aiki na 'Regular Recruit Intake 81'.

Don kauce wa zamba, hukumar tsaro ta saukaka lamarin ta hanyar samar da cibiyoyin daukar ma'aikata na zahiri a dukkan jihohi 36 na tarayyar da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT).

An fara daukar ma’aikatan ne a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli, kuma za a rufe a ranar Asabar, 24 ga watan Yuli, a cewar rundunar.

Kara karanta wannan

Shekaru bayan da aka zargi Dino Melaye da digirin bogi, ya bayyana yin digiri na biyu

Ga mai sha'awa, ga jerin dukkan cibiyoyin daukar ma'aikatan da aka samar:

Dalla-dalla: Ayyukan gwamnati da ake cikawa a yanzu, da yadda ake cikawa
Cibiyoyin da aka samar | Hoto: legit.ng
Asali: Facebook

Sojin Sama na Najeriya

Hakanan Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) tana neman wadanda suka kammala karatunsu na digiri da wadanda suka kammala karatunsu na digirgir domin a horar da su a matsayin 'Cadets Service Short Cadets'.

Za a bude kafar yanar gizo ta aika takardun neman aikin a ranar Litinin, 26 ga Yuli, kuma za a rufe ta Litinin, Agusta 30.

Ga masu sha'awar neman wannan aikin, ba kwa bukatar ziyartar kowane dandamali na kafofin sada zumunta. Abinda ya kamata kuyi shine ka ziyarci kafar yanar gizo ta NAF.

Hakanan masu sha'awar neman za su iya kiran wadannan layukan domin agaza musu a inda suka shige duhu daga 9:30 na safe zuwa 5:30 na yamma, Litinin zuwa Juma'a, 09064432351, 08043440802, 09055840142 ko Email: caeers@airforce.mil.ng idan ana bukatar karin bayani.

Dole ne su kuma lura cewa kyauta ne cika wannan aiki. Ga mai bukata, dole ne ka kasance dan asalin Najeriya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Dole ne ka kasance tsakanin shekarun 20 zuwa 30 kafin 30 ga Satumba 2022. Wadanda ke neman matsayi a harkar likitocin gidan soji, dole ne su kasance tsakanin shekaru 25 - 40.

Danna nan ko a nan don cikakken jerin abubuwan da ake bukata don neman aikin.

Dalla-dalla: Ayyukan gwamnati da ake cikawa a yanzu, da yadda ake cikawa
Daukar aiki a sojin sama | Hoto: legit.ng
Asali: Facebook

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC)

Hakanan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) tana daukar ma'aikata musamman ga mukamai uku:

  1. Officer cadre
  2. Marshal inspectorate (MI) cadre
  3. Road marshal assistant cadre

Don neman wannan aiki, ziyarci kafar yanar gizo ta FRSC, www.recruitment.frsc.gov.ng.

Ana sa ran masu neman mukamin 'Officer cadre' su mallaki digiri na farko, takardar shaidar kammala NYSC, kuma dole ne su zama basu wuce shekaru 30 ba.

Danna nan don samun cikakken jerin abubuwan da ake bukata don neman aikin.

Dalla-dalla: Ayyukan gwamnati da ake cikawa a yanzu, da yadda ake cikawa
Daukar aiki a hukumar kiyaye hadurra | Hoto: legit.ng
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

A wani labarin, Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel