Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

  • 'Yan bindiga sun sace Adogu na Eganyi, Alhaji Mohammed Adembe a jihar Kogi
  • Masu garkuwa da mutanen sun sace basaraken ne a a hayarsa na zuwa Eganyi daga Okene
  • Kakakin yan sandan jihar Kogi, Mr William Ayah, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa sunyi kokarin ceto shi

An yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya a Kogi
Taswirar Jihar Kogi. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun ƙwayoyi

Sace basaraken na zuwa ne kwanaki uku bayan sace wani kwararren masanin kimiyyan magunguna, AbdulAzeez Obajimoh, shugaban kamfanin magunguna na AZECO Pharmaceutical da ke Ozuwaya a Okene, yankin Kogi Central.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

Sace masanin magungunan da rana tsaka ya yi sanadiyar rasuwar wani matashi Habeeb Anda yayin da wasu biyu suka jikkata yayin da suka yi kokarin takawa masu garkuwar birki.

Wani majiya, da ya yi magana da manema labarai a waya, ya ce basaraken shi kadai ya ke cikin motarsa a hanyarsa na zuwa Eganyi daga Okene misalin karfe 4 na yamma amma yan bindigan suka sace shi tsakanin Ebiya da Eganyi.

Majiyar wadda ba a bayyana sunanta ba ta kara da cewa masu garkuwar sun kira iyalan basaraken misalin karfe 1 na ranar Laraba 14 ga watan Yulin sun nemi a biya Naira Miliyan 30 domin a fanso shi.

Rundunar Yan sanda ta tabbatar da sace Alhaji Mohammed Adembe

Kakakin yan sandan jihar Kogi, Mr William Ayah, ya tabbatar da lamarin yana mai cewa a tura tawaga ta musamman domin bin sahun masu garkuwan.

Ya yi kira ga jama'a da su taimakawa yan sanda da bayanai masu amfani da za su taimakawa jami'an tsaro ceto basaraken daga hannun yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun Ƙwayoyi

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin mai kama da wannan, yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel