Kungiyar IPOB ta kashe sojoji biyu a Enugu — Kakakin Soji

Kungiyar IPOB ta kashe sojoji biyu a Enugu — Kakakin Soji

  • An zargi bangaren tsaron kungiyar IPOB da kisan sojojin Najeriya guda biyu ranar Talata
  • Sojojin sun rasa rayukansu ne yayin musayar wuta da mayakan kungiyar IPOB
  • Ana fargabar hare-haren da kungiyar ke kai wa jami’an tsaron gwamnati sun fara dawowa

Ana zargin sashen tsaro na kungiyar IPOB (ESN), ya kashe sojoji biyu a Enugu.

A cewar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar, an kashe sojojin ne a ranar Talata a wani shingen binciken ababan hawa a Karamar Hukumar Uzo-Uwani na jihar, rahoton TheCable.

Ya ce mambobin kungiyar ta ESN sun yi artabu da sojojin a tsakanin su wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin, riwayar Guardian.

Yace:

"Sojojin Najeriya da aka tura domin dakile ayyukan 'yan bindiga a garin Adani na Karamar Hukumar Uzo-Uwani a Jihar Enugu, a jiya 13 ga watan Yulin 2021, sun mayar da martanin harin da sashen tsaro na kungiyar IPOB ya kai kan sojojin a wurin binciken ababen hawa da ke Iggah/Asaba"

Kara karanta wannan

Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

“Sai dai abin takaici, a lokacin artabun da ya faru, sojoji biyu sun ce ga garinku nan. A halin yanzu sojojin suna kan bin sahun masu aika-aikar.
“Muna tabbatar wa da sauran al’umma kudurinmu na samar da isasshen tsaro a yankin baki daya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Kungiyar IPOB ta kashe sojoji biyu a Enugu — Kakakin Soji
Kungiyar IPOB ta kashe sojoji biyu a Enugu — Kakakin Soji
Asali: Depositphotos

DUBA NAN: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka

A watannin baya sashen mayakan IPOB ya kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin tsaro da kadarorin gwamnati yankin Kudu maso Gabas.

Hare-haren sun tsagaita ne bayan kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ta IPOB, inda aka tasa kyayarsa zuwa Najeriya.

Amma da alama hare-haren na neman sake kunno kai.

Jami'an tsaro na yiwa matasanmu kisan gilla, Dattawan Igbo

A bangare guda, Shugaban kungiyar dattawa Igbo, kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Cif Chukwuemeka Ezeife, ya ce matasa da dama, akasarinsu maza, ana kashe su ba bisa ka'ida ba a kowace rana daga jami'an tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu

Ya bayyana hakan ne yayinda yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, rahoton ChannelsTV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel