'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

  • Masu garkuwa da mutane sun sace matar tsohon ciyaman din karamar hukumar Kaugama a Jigawa
  • Aliyu Ahmad, dan matar da aka sace ya tabbatar da lamarin yana mai cewa yan bindigan su kimanin 10 ne suka zo gidansu kan babura
  • Lawan Shisu, mai magana da yawun yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da lamarin yana mai cewa sun bazama neman masu garkuwar

'Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace matar tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa
Taswirar Jihar Jigawa: Hoto: Channels TV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jerin Sunayen Sakatarorin Dindindin 5 da Buhari Ya Rantsar

Dan matar da aka sace ya yi bayanin yadda lamarin ya faru

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Matar da aka sace sunanta Hajiya Fatima, uwargidan tsohon shugaban karamar hukumar.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

KU KARANTA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Ya kara da cewa wadanda suka sace tan sun tuntube su amma ba su nemi a biya kudin fansa ba.

Ya ce:

"Hudu cikin yan bindigan suka shiga gidan mahaifinmu, yayin da shida cikinsu suka tsaya a waje.
"Sun yi wa matan da ke gidan duka sannan suka yi awon gaba da mahaifiyata a kan babur dinsu.
"Sun kira mu amma ba su riga sun fada adadin abin da suke son a biya ba kafin su sako ta ba. Mun kai wa yan sanda a Kaugama rahoton abin da ya faru."

Yan sanda sun bazama neman masu garkuwar

Kara karanta wannan

Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi

Kakakin yan sandan jihar, Lawan Shisu, shima ya tabbatarwa The Channels lamarin.

Ya bada tabbacin cewa yan sanda da yan banga da mafarauta a garin suna kokarin bin sahun masu garkuwar domin kama su tare da ceto wacce aka sace.

Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun ƙwayoyi

A wani rahoton daban, Rundunar yan sandan jihar Imo ta ce ta kama Nnamuka Uchenna, wani da ake zargi dillalin miyagun ƙwayoyi ne da ke sayarwa mambonin kungiyar IPOB da ESN kwayoyi, rahoton The Cable.

SaharaReporters ta ruwaito cewa an kama Uchenna ne a gidansa da ke Umuaka a ƙaramar hukumar Njaba a ranar 8 ga watan Yuli inda aka gano wasu abubuwa da ake zargin hodar Iblis ne da kudinsu ya kai Naira miliyan 150.

An kama shi ne tare da wani Chinedu Ukaegbulam da Augustine Ete.

Asali: Legit.ng

Online view pixel