Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mambobin majalisar dokokin Najeriya a jiya Talata
  • Rahotanni sun bayyana abubuwa masu muhimmanci da shugaban kasan ya tattauna dasu
  • A yayin zaman liyafar, shugaba Buhari ya fadi wasu abubuwa masu muhimmanci guda hudu

A yammacin jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mambobin majalisar dokoki ta kasa, domin gudanar da wata liyafa.

Shugaban kasar ya tattauna da 'yan majalisu da sanatocin, yayin da ya bayyana wasu maganganu ciki har da yabo da ba da tabbaci da goyon baya a gwamnatinsa.

Hakazalika, jaridar Punch ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu ya bayyana matsalolin da kasar ke fuskanta, inda ya nemi goyon baya wajen magance su.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Bayan dogon cece-kuce, majalisa ta karbi rohoton gyara dokar zabe

Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu
Mambobin Majalisar Dokoki yayin liyafa | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

A takaice, ga abubuwan da shugaban ya magantu a kai yayin liyafar:

Batun rashin tsaro

Shugaba Buhari ya yi magana a kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya, inda ya ce ita ce matsala daya tilo mafi wahala da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro take shafar ayyukan gwamnati na yin abubuwan more rayuwa, da samar wa mutane bukatunsu da kuma hana masu zuba jari walwala da samar da masana'antu da samar da ayyukan yi, BBC Hausa ta ruwaito.

''Wasu daga cikin mutanen da suke jawo matsalar rashin tsaron nan suna yi ne bisa son ransu, ba tare da wani dalili ba.
''Ko ma dai mece ce manufarsu, to ayyukansu barazana ne ga kasarmu.

Buhari ya ce zai iya komai don kawo karshen matsalar tsaro

Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnatinsa a shirye take ta yi komai don kawo karshen matsalar tsaro a kasar tare da gurfanar da masu laifin a gaban hukuma.

A cewarsa:

''A wannan yanayin, dole ne mu yi komai da za mu iya, ba tare da mun bari wani abu ya dauke min hankali ba, don kawo ƙarshen ayyukansu.
''Ba za mu bari wani abu ya dauke mana hankali daga wannan muradin ko dakile kokarinmu ba, kuma ina da kwarin gwiwar cewa za mu yi nasara tare a wannan kokarin."

Kara karanta wannan

Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

Shugaba Buhari ya yabi Majalisar Dokoki

A wajen taron Shugaba Buhari ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin kasar ta tara kan yadda take gudanar da ayyukanta cikin "nuna girma da kwarewa, yana mai bayyana 'yan majalisar da "abokan hulka wajen gina kasa."

Sannan ya yabi jam'iyyun adawa a majalisar kan hadin kan da suke bayarwa wajen shirye-shiryen gwamnati.

Ya ce:

''Samun damar shugabancinmu don kyautata wa 'yan Najeriya ya danganta ne da irin hadin gwiwa da za mu yi da bangaren dokoki da bangaren zartarwa.
''Sa ido kan duba abin da kowane bangare ke ciki ba zai zama gayyatar fada ba, kuma ba zai zama cacar baki a lokacin tattaunawa don neman shawara ba.

Nasarorin da Majalisar Dokoki ta samu

Haka kuma shugaba Buhari ya bayyana wasu nasarori da Majalisar Dokokin ta tara ta samu, kamar dawo da lokacin kasafin kudi daga watan Janairu zuwa na Disamba.

Da yin kwaskwarima ga kudurin dokar kamfanoni CAMA, da dokar 'yan sanda da dokar kudi da sauransu.

Kara karanta wannan

Kasar Kamaru ta taya Buhari murna bisa nasarar kame Nnamdi Kanu, ta bayyana dalili

Sannan ya yabi shugabancin majalisun biyu karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan da shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, saboda sadaukarwarsu a lokacin da ake fusantar matsaloli.

KARANTA WANNAN: Korona: NCDC ta gargadi Musulmai game da yawon babbar sallah, ta fadi sharudda yawo

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana gwamnatin APC a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi kyawun gwamnatin da Najeriya ta taba yi tun bayan ayyana kasar a shekarar 1914 da Turawan mulkin mallaka suka yi.

Ya gargadi sassan Najeriya game da abinda ya bayyana a matsayin rashin adalci kan gwamnatin Shugaba Buhari, yana mai cewa ya kamata 'yan Najeriya su yaba duba da matsalar tattalin arziki da gwamnatin ke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta a 2015.

Kara karanta wannan

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Ya ta'allaka matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel