Cikakken bayani: Bayan dogon cece-kuce, majalisa ta karbi rohoton gyara dokar zabe

Cikakken bayani: Bayan dogon cece-kuce, majalisa ta karbi rohoton gyara dokar zabe

  • Bayan cece-kuce da ya dinga yawo game da kudurin gyara dokar zabe, majalisa ta karbi rahoto a kai
  • Majalisar ta karbi rahoton ne a yau Laraba 14 ga watan Yuli 2021, kuma za ta zauna don tattauna batun
  • Kakakin majalisa Femi Gbajabiamila ya ba da tabbacin cewa, majalisar za ta karanta batun

Bayan kwanaki ana ta cece-kuce, Majalisar Wakilai a ranar Laraba ta karbi rahoton Kwamiti kan Al’amuran Zabe kan kudirin dokar gyaran dokar zabe, The Nation ta ruwaito.

Wasu bayanan da ake zargi na rahoton sun kasance cikin cece-kuce tsakanin al'umma fiye da mako guda, wanda ya tilasta shugabancin majalisar bayyana dagewarta cewa har yanzu bata karbi rahoton Kwamitin ba.

KARANTA WANNAN: Korona: NCDC ta gargadi Musulmai game da yawon babbar sallah, ta fadi sharudda

Da duminsa: Majalisa ta karbi rohoton gyara tsarin dokar zabe bayan cece-kuce
Majalisar wakilai a Najeriya | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

An gabatar da rahoton ne a gaban majalisar daga shugaba na kwamitin Al'amuran Zabe, 'yar majalisar wakilai, Aisha Jibril Dukku.

Kara karanta wannan

Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari

Ana sa ran za a duba rahoton ne a ranar Alhamis kafin majalisar ta fara hutun bazara na shekara-shekara.

Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya bada tabbacin majalisar za ta zartar da kudirin kafin hutun bazata.

Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC

A jiya kuwa, majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.

An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.

KARANTA WANNAN: Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Kara karanta wannan

N700m na rashawar Diezani: EFCC ta sake gurfanar da Yero tare da sauran

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana gwamnatin APC a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mafi kyawun gwamnatin da Najeriya ta taba yi tun bayan ayyana kasar a shekarar 1914 da Turawan mulkin mallaka suka yi.

Ya gargadi sassan Najeriya game da abinda ya bayyana a matsayin rashin adalci kan gwamnatin Shugaba Buhari, yana mai cewa ya kamata 'yan Najeriya su yaba duba da matsalar tattalin arziki da gwamnatin ke fuskanta tun lokacin da aka kafa ta a 2015.

Ya ta'allaka matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta da faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya, Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel