Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi

Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi

  • Sarki Alhassan Adamu ya fashe da kuka a gaban mutane bayan da masu satar mutane suka sake shi a jihar Kaduna
  • Yayin da mutumin mai shekaru 85 ke cikin hawaye, mutanen da suka ziyarce shi sun tausaya masa yayin da suke lallashin dattijon
  • An sace mutumin kwanakin baya tare da wasu daga cikin iyalinsa da tsakar dare

Wani faifan bidiyo ya nuno mai martaba sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, mai shekaru 85, a cikin jihar Kaduna yana zubar da hawaye lokacin da aka kubutar da shi daga kogon masu satar mutane.

Ku tuna cewa an sace sarkin a gidansa da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

Bidiyo ya nuna lokacin da mai martaba sarkin Kajuru ya fashe da kuka bayan masu satar mutane sun sako shi
Sarkin ya fashe da kuka yayin da yake jawabi Hoto: The Punch Newspaper
Asali: UGC

Satar nasu

A cewar Jaridar Punch, masu laifin sun kuma sace wasu iyalan sarkin 12 da suka hada da mata da yara.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Jikan sarki kuma mai rike da sarautar Dan Kajuru, Saidu Musa ya tabbatar da satar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa ta amince da daurin shekaru 20 ga barayin akwatin zabe

Yayin wata ziyarar girmamawa da aka kai masa, sarkin ya fashe da kuka jim kadan bayan ya ce:

"Jama’ar Kajuru, ina yi muku barka da saduwa da ni."

Kalli bidiyon da Punch ta wallafa a Facebook a kasa:

'Yan Najeriya sun nuna matukar damuwa

Femi Adewusi ya ce:

"Shugabannin Arewa, na gargajiya da na siyasa, suna girbe abun da suka kwashe shekaru suna yi wa Talakawa masu rinjaye da yaudarar addini ..."

Ahmed-Laotan Sulaimon ya ce:

"Waɗanda suka ga zuwan hakan amma suka yi gargaɗi da ƙyar ake bari su dade a matsayin sarki. Abu ne ya tabarbare, Rikicin da duk kuka kirkira. Ka daina kuka Ya Mai Martaba Sarki!!!! "

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi biyu ne kawai ke cikin aminci a Kaduna - Sanata Sani

A wani labarin, Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna, ya bayyana cewa yana cikin matuƙar damuwa saboda halin ƙunci da al'umar Kaduna suke ciki wanda matsalar tsaro ta haifar a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

A jawabin da gwamnan yayi lokacin gabatar da rahoton tsaro kashi na 2 a cikin 2021, El-Rufa'i yace wannan rahoton ya bayyana komai game da halin da mutane suke ciki.

"Wannan adadin da rahoton tsaro kashi na 2 a cikin 2021 ya gano, ya nuna ƙarara irin halin ƙuncin da al'umma suke ciki, baƙin ciki, rashin yan uwansu da tsoron da aka jefa su a ciki," inji gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel