Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu

Da Dumi-Dumi: Yan Ta'addan ESN-IPOB Sun Ragargaji Sojoji da Dama a Jihar Enugu

  • Wasu yan bindiga da ake zargin yan ƙungiyar ESN-IPOB ne sun kaiwa sojoji hari a jihar Enugu
  • Rahotanni sun bayyana cewa an yi gumurzu sosai, kuma sanadiyyar haka sojoji biyu suka rasa rayukansu
  • Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da harin, ta bayyana cewa jami'anta sun bi sawun maharan

Wasu yan bindiga sun kashe sojoji shida a Adani, karamar hukumar Uzo-Uwani, jihar Enugu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka da Ta Yi Wuf da Dan Najeriya, Ta Canza Suna

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe sojojin ne da safiyar Talata, a madakatar duba abun hawa dake kan babbar hanyar Nsukka-Adani-Anambra.

Rahoton channels tv ya nuna cewa, Lamarin ya faru ne yayin da sojojin suka yi ƙoƙarin fatattakar yan bindigan, waɗanda ake zargin mayaƙan ESN-IPOB ne, a wajen binciken abun hawa dake Iggah/Asaba.

Jami'an rundunar sojin ƙasa
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji da Dama a Enugu Hoto: dw.com
Asali: UGC

Rundunar soji ta tabbatar da kai harin

Kara karanta wannan

Hotunan Wata Kyakkyawar Budurwa Yar Amurka Ta Yi Wuf da Dan Najeriya, Ta Canza Suna

Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta tabbatar da kai harin, amma ta bayyana cewa sojoji sun bi sawun yan ta'addan.

Kakakin rundunar sojin ƙasa, Onyema Nwachukwu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya fitar, yace lamarin ya faru ne yayin da jami'an soji suka yi ƙoƙarin daƙile wani hari a Iggah/Asaba.

Yace: "Sojojin Najeriya da aka tura domin su binciki ayyukan yan bindiga a yankin Adani, ƙaramar hukumar Uzo-Uwani Jihar Enugu, a jiya 13 ga watan Yuni sun daƙile harin yan ta'addan ESN a madakatar Iggah/Asaba"

"Abin takaincin shine yayin fafatawarsu da maharan jami'an soji guda biyu sun rasa rayuwarsu. A halin yanzu sojoji sun bazata nemo waɗanda suka kai wannan harin."

KARANTA ANAN: Bikin Babbar Sallah: Mutane sun Koka Kan Yadda Farashin Dabbobin Layya Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Zamu tabbatar da tsaro

Rundunar sojin ta tabbatar wa mutanen yankin cewa ba zata gajiya ba sai ta tabbatar da tsaro tare da taimakon sauran hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Ina mamakin yadda yan Najeriya suka zabeni duk da ban da kudi, Buhari

Hakazalika, rundunar ta roƙi al'umma da su cigaba da kasancewa masu bin doka sau da ƙafa, kuma su taimakawa jami'an tsaro da sahihin bayani game da yan ta'adda.

A wani labarin kuma Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, ya lallashi wasu mutanen jiharsa kan yadda hanyoyi suka lalace.

Gwamnan ya yi wannan magana ne yayin da yake kaddamar da yaƙin neman zaɓen APC a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel