Kasar Kamaru ta taya Buhari murna bisa nasarar kame Nnamdi Kanu, ta bayyana dalili

Kasar Kamaru ta taya Buhari murna bisa nasarar kame Nnamdi Kanu, ta bayyana dalili

  • Jamhuriyar Kamaru ta bayyana farin cikinta bisa kame Nnamdi Kanu, tana mai tura sako ga shugaba Buhari
  • Ta bayyana cewa, ita ma tana fuskantar irin wannan matsala ta neman ballewa daga wata kungiya a kasar
  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa, zai ba da goyon bayan da ake bukata domin tabbatar da zaman kasar a dunkule

Hukumomin Kamaru sun taya Najeriya murna game da kamun Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ta'addanci ta IPOB, Today.ng ta ruwaito.

Mista Felix Mbayu, Dan aike na Musamman daga Shugaba Paul Biya na Kamaru, ya taya Najeriya murna lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbe shi a Abuja ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Dalilai da suka sanya majalisar dattawa ta ki amincewa da nada Onochie a INEC

Kasar Kamaru ta taya Buhari murna bisa nasarar kame Nnamdi Kanu, ta bayyana dalili
Shugaba Buhari a ziyara kasar Kamaru | Hoto: prc.cm
Asali: UGC

Ya ce Paul Biya ya sa ido kan halin da Najeriya ke ciki, da fatan ba zai samu ba ga kungiyar Ambazonian da za ta dagula kasar Kamaru, “kamar yadda wasu mutane ke amfani da rikice-rikicen da ke faruwa a bangarorin biyu na masu magana da turanci da ke Kamaru don wargaza kasar.”

Kara karanta wannan

Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

Kamar IPOB, Ambazonia na neman ballewa daga Kamaru.

Shugaban kasar Kamaru ya yi farin ciki da kame Nnamdi Kanu

Mista Mbayu, wanda kuma shi ne Ministan Hadin gwiwar Hadin Kai da Kungiyar Kasashe, ya ce Shugaba Biya ya yi farin ciki da rawar da Najeriya ke takawa a Afirka.

Ya ce makwabtan biyu ba su hada kan iyakoki da alakar tarihi kadai ba, sun hada "har ma da kalubale iri daya."

Ya kara da cewa:

"Wadannan kalubalen sun shafi tsaro musamman, kuma ya zama wajibi akanmu mu nemi mafita baki daya."

Buhari, yayin da yake magana, ya ce Najeriya za ta bayar da kyakkyawar goyon baya don tabbatar da cewa Jamhuriyar Kamaru ta kasance kasa da ba za ta rabu ba.

Shugaban, yayin da yake cewa Najeriya na sane da irin wannan hargitsi na ballewa daga kungiyar Ambazonian, ya kuma jaddada cewa yana da kyau ga Najeriya "a tabbatar da cewa Kamaru ta zauna lafiya, kuma za mu ci gaba da mara baya da ba da goyon bayan gare ku.

Kara karanta wannan

Ohanaeze ta fadawa Bello: Kana makaranta lokacin da Arewa da Kudu suka amince da karɓa-karɓa

Akwai dangantaka tsakanin Najeriya da Kamaru mai karfi - Shugaba Buhari

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar, ya ce Najeriya da Kamaru sun hada dangantakar tarihi da kan iyakoki guda biyu, wanda hakan ya zama wajibi ga kasashen biyu su kula da junansu, Daily Trust ta ruwaito.

“Wannan shine dalilin da ya sa lokacin da na fara mulki a shekarar 2015, nan da nan na ziyarci dukkan makwabtanmu, saboda mun kasance da alaka game da darajar kyakkyawar makwabta.

KARANTA WANNAN: Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

A wani labarin, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami (SAN), a ranar Litinin, 12 ga watan Yuli ya mayar da martani ga matsayar kungiyar koli ta zamantakewar al'adun Ibo, Ohanaeze Ndigbo, na sanya ido kan shari'ar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Malami, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Umar Gwandu kuma Legit.ng ta gani, ya yi maraba da kafa kungiyar lauyoyin da kungiyar ta yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel