Ohanaeze ta fadawa Bello: Kana makaranta lokacin da Arewa da Kudu suka amince da karɓa-karɓa

Ohanaeze ta fadawa Bello: Kana makaranta lokacin da Arewa da Kudu suka amince da karɓa-karɓa

  • Kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ya ragargaji Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi kan cewa tsarin karba-karba na shugabancin kasa ya saba wa doka
  • Kungiyar ta ce tun lokacin Gwamna Bello na jami'a a Zaria dattawan Arewa da Kudu suka yi taro suka amince da tsarin
  • Kungiyar ta kuma kara da cewa Gwamna Yahaya Bello mutum ne maras kaifin tunani wanda ya fada siyasa ba tare da tsari ba

Kungiyar kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta yi wa Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi martani kan cewa tsarin karba-karba na shugabancin kasa tsakanin Kudu da Arewa ya saba wa kundin tsarin mulki, The Punch ta ruwaito.

A jawabin da ya yi a ranar Juma'a da ta gabata yayin taron masu rahotanni na siyasa da laifuka karo na farko da aka yi a Abuja, gwamnan ya bayyana karba-karba a matsayin abin da ya saba wa doka, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Ohanaeze ta fadawa Bello: Kana makaranta lokacin da Arewa da Kudu suka amince da karɓa-karɓa
Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zamfara: Ba za mu bari abin da ya faru da APC a 2019 ya sake faruwa ba, Yeriman Bakura

Amma a martanin da ta yi jiya kamar yadda The Cable ta ruwaito, Ohanaeze cikin sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren watsa labaranta na kasa, Alex Ogbonnia, ta ce gwamnan yana kutse cikin siyasa ne amma ba shi da tsari ko zurfin tunani.

Ohanaeze ta ce:

"Gwamna Bello yana dalibi a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria yana karatun Akanta lokacin da Arewa da Kudu suka cimma yarjejeniyar yin karba-karba na shugabancin kasa tsakaninsu.
"A dakin taro na hukumar kula da jami'o'i na kasa da ke Abuja aka yi taro a 1998. Dr Chuba Okadigbo ya yi magana a madadin Kudu yayin da Alh. Abubakar Rimi ya yi magana a madadin Arewa. Irinsu Dr. Alex Ekwueme, Cif Solomon Lar, Dr. Okwesilieze Nwodo da sauransu sun hallarci taron.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello

KU KARANTA: Sojoji Sun Ceto Mutum 17 Bayan Ragargazan Ƴan Boko Haram a Borno

"Nigeria ta yi nazarin amfani da rashin amfanin yin karba-karbar tsakanin yankunan kasar. Daga karshe ta amince za a bawa kudu mulki sannan za a rika karba-karba tsakanin kudu da arewa domin adalci, dai-daito, hadin kai da cigabar Nigeria a matsayin kasa daya."

2023: Ku Dena Cewa Tilas Ne a Baku Mulki, Zulum Ya Gargaɗi Gwamnonin Kudu

A wani labarin daban, Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce ba dole bane kudancin Nigeria ta fitar da shugaban ƙasa na gaba, The Cable ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a matsayin martani kan matsayar da takwarorinsa na kudu suka yi.

Da ya ke martani kan cigaban, Zulum, yayin hira da aka yi da shi a Channels TV, ya jadada goyon bayansa ga Kudancin kasar na fitar da shugaban ƙasa amma ya gargadi amfani da kalmar 'dole' yayin tattaunawa batun.

Kara karanta wannan

Malami ya amince Inyamurai su sa ido kan shari'ar Nnamdi Kanu, amma da sharadi

Asali: Legit.ng

Online view pixel