'Yan bindiga sun bankado rashin tasirin hada lambobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

'Yan bindiga sun bankado rashin tasirin hada lambobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

  • ‘Yan bindigar sun bayyana rashin inganci da tasirin hada lambobin NIN da na SIM
  • An gano cewa jami’an tsaro ba sa wani katabus wajen bibiyar sawun miyagun mutane ta hanyar amfani da lambobin wayar ‘yan ta’addan
  • Na’urorin da ‘yan sanda ke amfani da su wajen bibiyar miyagun mutane sun lalace

Wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Litinin sun bayyana yadda ‘yan bindiga ke dakile matakan tsaro na Gwamnatin Tarayya a bangaren sadarwa.

Mazauna jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna wadanda suka baiwa jaridar Punch labarin irin abubuwan da suka fuskanta a wuraren da masu satar mutane suke, sun shaida wa manema labarai cewa sun bai wa jami’an tsaro lambobin wayar ‘yan bindigar.

Sai dai sun koka cewa, duk da hakan babu wani abin da aka yi domin kama miyagun, hakan ya sa ake ganin umarnin Gwamnatin Tarayya kan rajistar masu amfani da wayar tarho da kuma lambar shaidar kasa a zaman shiririta ce kawai.

Kara karanta wannan

UTME: Iyaye sun roke ni da in dafawa ’yayansu - Shugaban hukumar JAMB

Karkashin Sashe na 19 da 20 na Hukumar Sadarwa ta Najeriya (Rajistar masu amfani da Waya) a Dokokin shekarar 2011, ana sa ran kamfanonin sadarwar za su yi wa dukkanin masu amfani da salula rajistar.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

'Yan bindiga sun bankado rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga
'Yan bindiga sun bankado rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga
Asali: UGC

DUBA NAN: Yadda zamu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo

A shekarar 2015, hukumar NCC ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su datse layukan SIM din da ba su da rajista ko aka yi musu rajistar da ba ta kammala ba.

Dokar, a cewar gwamnati, an yi ta ne da nufin tabbatar da cewa ana iya bibiyar duk masu amfani da layukan wayar salula rajistar saboda dalilan tsaro.

A bara hukumar NCC ta ba da umarnin hada layukan SIM da NIN da zimmar kara inganta tsaro.

Amma wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda suka zanta da jaridar The PUNCH, sun ce lura da yadda 'yan bindigar ke ci gaba da sheke ayarsu, wadannan dokokin biyu ba su da wani amfani.

Kara karanta wannan

COVID-19: Yadda Najeriya ta kunyata masana - Aregbesola

A jihar Zamfara, wani da aka yi garkuwa da shi, Malam Yusha'u Jangebe, ya ce jami'an tsaro a kauyensu na Jangeme, ba su iya yin wani katabus ba wajen gano kiran wayar da 'yan ta'addan suka rika yi.

Jangebe ya ce 'yan ta'addan a watannin baya sun yi garkuwa da mutum bakwai a kauyensu kuma an tuntube shi ya kawo kudin fansa kafin a sake su.

A cewarsa, lokacin da ya isa dajin domin bai wa masu satar mutane N1.4m cikin N3m da suka nema, sai suka tsare shi suna cewa dole ne ya kawo sauran cikon N1.6m.

Ya ce,

"Jami'an tsaron da aka tura kauyenmu (Jangebe) sun san abin da ke faruwa, amma ba su yi wani yunkurin amfani da lambar wayar da 'yan fashin da suka sace mu suka aiko ba.”

Da yake amsa zargin da ake yi cewa ‘yan sanda ba sa son bibiyar ‘yan bindigar bayan sun samu bayanai daga dangin wadanda aka sace, kakakin rundunar, Frank Mba, ya ce,

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

“Ba a yin binciken manyan laifuka irin wannan a bayyane. A tsarin aiki yadda ya dace, irin wadannan binciken cikin sirri ake yin su da leken asiri cikin manufa.”

Gwamnatin tarayya zata fara bibiyan Whatsapp din yan Najeriya

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta ajiye kimanin bilyan 4.8 ga hukumar leken asirin Najeriya (NIA) domin bibiyan abubuwan da yan Najeriya ke tattaunawa a WhatsApp da kuma salular Thuraya.

WhatsApp wata manhaja ce da mutane ke tattaunawa da 'yan uwa da abokan arziki.

WhatsApp mallakin kamfanin Facebook ne dake jihar California a Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel