Da dumi-dumi: Jerin sunayen kwamishinonin INEC 5 da majalisar dattijai ta tabbatar da su

Da dumi-dumi: Jerin sunayen kwamishinonin INEC 5 da majalisar dattijai ta tabbatar da su

  • Majalisar dattawan Najeriya ta amince da wasu mutane biyar a matsayin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta
  • Wadanda aka tabbatar sune Farfesa Muhammad Sani Kallah; Farfesa Kunle Ajayi, Saidu Ahmad, Baba Bila da Abdullahi Zuru
  • Har ila yau majalisar ta ki tabbatar da Farfesa Sani Adam daga Arewa ta Tsakiya saboda koke-koken da ake yi a kansa

Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin Kwamishinoni biyar a hukumar zaben kasar, jaridar Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa majalisar tarayyar ta tabbatar da zabin na Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne bayan nazarin rahoton kwamitinta a kan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, a ranar Talata, 13 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

Da dumi-dumi: Majalisar dattawa ta amince da nadin kwamishinonin zabe 5, ta ki tabbatar da Adam
Majalisar dattawa ta amince da nadin kwamishinonin zabe biyar Hoto: @DrAhamdLawan1
Asali: Facebook

Jerin sunayen kwamishinonin kasar da aka tabbatar

1. Farfesa Muhammad Sani Kallah (Katsina)

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata

2. Farfesa Kunle Ajayi (Ekiti)

3. Saidu Ahmad (Jigawa)

4. Baba Bila (Arewa Maso Gabas)

5. Abdullahi Zuru (Arewa maso Yamma).

A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa, bayan shawarar da kwamitinta ya bayar, ta ki tabbatar da Farfesa Sani Adam daga Arewa ta Tsakiya saboda koke-koken da ake yi a kansa.

Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC

A baya mun ji cewa Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC

An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel