Yanzu-yanzu: PDP ta je kotu, ta nemi a kwace kujerar gwamna Matawalle da mataimakinsa

Yanzu-yanzu: PDP ta je kotu, ta nemi a kwace kujerar gwamna Matawalle da mataimakinsa

Jam’iyyar PDP ta nemi wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta kori Gwamnan Zamfara da Mataimakinsa - Bello Muhammad Matawalle da Mahdi Aliyu Gusau - kan ficewarsu daga Jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC, The Nation ta ruwaito.

Bukatar tana daga cikin abinda PDP ta nema a wata kara mai lamba: FHC / ABJ / CS / 489/2021 da aka gabatar da sunayen mambobin PDP biyu daga jihar Zamfara - Sani Kaura Ahmed da Abubakar Muhammed.

Masu shigar da karar suna kalubalantar cewa, saboda hukuncin da Kotun Koli ta yanke a baya, kan cewa APC ba ta da wani dan takara a zaben gwamna a 2019 a Jihar Zamfara, ba ta gudanar da zaben fidda gwani ba.

Yanzu-yanzu: PDP ta je kotu, ta nemi a kori gwamna Matawalle da mataimakinsa
Gwamna Matawalle da Mataimakinsa Gusau | Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

A cewarsu, duba da wancan hukunci, ya haramta ga Matawalle da Gusau su rike ofisoshinsu yayin da suka fice daga PDP zuwa APC, kuma ta hakan suka canza nasarar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa: Yeriman Bakura ya magantu kan tsayawa takara a 2023 karkashin APC

Suna son kotu ta bayyana cewa dole ne Matawalle da Gusua su yi murabus daga ofisoshinsu kafin ficewarsu don ba Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) damar gudanar da sabon zabe, cikin watanni uku, don PDP ta maye gurbinsu.

Karin bayanin yadda ta kaya na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel