Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

Dr Isa Ali Pantami: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah

  • Tsokacin Edita: Watan Zul-Hijjah wata ne na 12 a watannin muslunci, wadanda suke fara lissafi daga hijirar Annabi Muhammadu SAW daga Makkah zuwa Madina. A wannan watan ne ake aikin Hajji, wanda rukuni ne daga cikin rukunnan muslunci.
  • Musulman duniya na taruwa a kasar Makkah mai alfarma domin gudanar da ayyukan Hajji, yayin da sauran musulman duniya dake wasu kasashe ke kokarin aikata ayyukan ibada domin neman samun kusanci da Allah madaukakin darki.
  • A kwanaki 10 na farkon watan Zul-Hijja, malamai na kwadaitar da ilahirin musulmin duniya wajen yawaita ayyukan alheri kama daga azumi har zuwa ciyarwa da dai sauran nau'ikan ibadu wadanda suke na nafila

Babban malamin addinin Islama, kuma minista na sadarwa a Najeriya, Sheikh Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ja hankalin musulmin duniya kan yawaita ayyukan alheri a cikin wannan wata na Zul-Hijja.

A cikin wani bidiyo da ya watsa a shafinsa na Facebook, wanda Legit.ng Hausa ta samu, malamin ya bayyana falalar dake tattare da watan Zul-Hijja, ya kuma shawarci jama'ar musulmi da su yi kokarin amfana da wadanann kwanaki masu daraja.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyon Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana

Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hijjah Daga Sheikh Dr. Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami | Hoto: technopreneur.com
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Cikakken Bayani: Bayan Sace Sarkin Kajuru, An Sako Ma'aikatan Lafiya da Aka Sace a Yankin

Da yake bayyana falalar kwanakin, ya kawo Hadisi, ya ce Annabi SAW ya ce:

"Babu wasu kwanaki da ayyuka na kwarai yake soyuwa a wurin Allah SWT fiye da wadannan kwanaki."

Hakazalika, ya ce wasu malamai suna kan ra'ayin cewa, wuni goma na farkon watan Zul-Hijja sun fi falala akan wuni goma na karshen watan Ramadana, kamar yadda darare goma na karshen watan Ramadana suka fi darare goma na farkon watan Zul-Hijjah.

Malamin, ya kuma bayyana cewa, Hadisi ya inganta babu ayyukan da suka fi falala, tsarki da lada a wurin Allah fiye da ayyukan da aka yi su cikin kwanaki goma na farkon watan na Zul-Hijjah.

Abubuwan da ake so musulmi ya yi a wadanann kwanaki goma na Zul-Hijja

1. Duk wanda zai yi yankan layya, kada ya aske gashin kansa, kada kuma ya yanke farce har sai an yi babbar Sallah

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

2. Ana son musulmi su yawaita yin azumi a kwanaki na farkon watan Zul-Hijjah, saboda Annabi yakan azumci kwanaki tara na farkon watan Zul-Hijjah.

3. Ana son musulmi ya yawaita yin tasbihi, ma'ana yawaita fadin 'Allahu Akbar, wa Subhanallah, wal Hamdu liLlah'

4. Ana son wanda yake da hali ya yi yankan layya ranar goma ga watan.

5. Ana son a yawaita ba da sadaka

6. Ana son a yawaita karanta al-Kur'ani

7. Ana son a yawaita gaida marasa lafiya

8. Yin sulhu tsakanin musulmai

9. Da sauran ayyukan lada

Kalli cikakken bidiyon:

KARANTA WANNAN: Murna: Hotunan Atiku da Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Lokacin da Ta Kammala Digiri

Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa

A wani labarin, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana cewa, a yi masa afuwa kuma lallai ya janey maganganun da ya yi game Manzon Allah SAW wadanda ake ganin sun taba mutuncin ma'aiki.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Dakatar da Kungiyar Masu Bashi Shawari Na Musamman Saboda Rikicin Cikin Gida

A cikin wani sauti karo na biyu da ya aike wa sashen Hausa na BBC ranar Lahadi, malamin ya ce yana fatan "hakan ya zama silar gafara da rahama da jin kai gare ni".

Ya kara da cewa: "Wadannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma'aiki SAW, na janye su na kuma janye su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel