Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu

  • Fittacen mawakin Nigeria, Olanrewaju Fasasi, da aka fi sani da Sound Sultan ya mutu
  • Marigayin ya mutu ne yana da shekaru 44 a duniya bayan ya yi jinyar ciwon kansa ta makogoro
  • Sound Sultan ya rasu ya bar matar aure daya da yara guda uku

Olanrewaju Fasasi, tauraron mawaƙin Nigeria, da aka fi sani da Sound Sultan ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, iyalan mawakin sun ce ana masa maganin cutar kansa na moƙogoro ne kafin rasuwarsa.

The Punch ta ruwaito an fara yi wa mawaƙin maganin kansa ta Chemotherapy ne tun a watan Mayu.

DUBA WANNAN: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu
Yanzu-Yanzu: Shahararren mawaƙin Nigeria, Sound Sultan ya mutu
Asali: Original

Sound Sultan ya fara harkar waƙa ne tun a shekarun 1990s, a lokacin da ya ke gabatar da shirye-shirye domin ya samu kudin da za a naɗa masa waƙa.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

Ya fitar da wakar 'Jagbajantis' a shekarar 2000 wacce ta yi fice sosai a lokacin.

Bayan ya fitar da wasu wakokin da kansa tare da wasu mawakan, ya rattaba hannu kan kwantiragi da kamfanin Kennis Music inda ya fitar da album na wakoki hudu.

Sound Sultan ya fara aiki tare da mawakin Amurka Wyclef Jean bayan ya yi waka tare da 2face Idibia da Faze a wakar 'Proud to be African'.

KU KARANTA: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

A shekarar 2012, An nada Sound Sultan matsayin wakilin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, UN, saboda 'rayuwa ta dattaku' da nasarar da ya samu a sana'arsa.

A 2015, Sound Sultan ya fitar da wakar 'Remember' bayan ya dade bai fitar da waka ba.

An haifi shi ne a ranar 29 ga watan Nuwamban 1976, ya kuma rasu ya bar mata daya da 'ya'ya uku.

Kara karanta wannan

Wani babban Jigon PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Shugaban Hukumar NCFRMI Na Kano, Zeenat Kaltume-Yahaya, Ta Rasu

A wani labarin, shugaban hukumar kula da yan gudun hijira da wadanda suka rasa muhallinsu, NCFRMI, na jihar Kano, Mrs Zeenat Kaltume-Yahaya, ta rasu tana da shekaru 48, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai bada shawara na musamman kan kafafen watsa labarai na kwamishinan NCFRMI, Sadiq Abdullateef, wanda ya bada sanarwar a ranar Juma'a, ya ce Kaltume-Yahaya ta rasu a daren Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya.

A sakon ta'aziyyar, kwamishinan dai-daito na NCFRMI, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana marigayiyar a matsayin ma'aikaciya mai jajircewa wurin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel