Matasan Tibi Sun Yabawa Buhari Kan ‘Ragargazan’ Nnamdi Kanu da Sunday Igboho

Matasan Tibi Sun Yabawa Buhari Kan ‘Ragargazan’ Nnamdi Kanu da Sunday Igboho

  • Kungiyar matasan kabilar Tibi, ta yabawa Shugaba Buhari kan kama Nnamdi Kanu da kaiwa Sunday Igboho samame
  • Kungiyar ta ce babu wata kasa da za ta zuba wa bata gari da yan ta'adda ido su tara makamai da tada rikici
  • Kungiyar ta ce ya kamata duk wani mai kishin kasa ya mara wa shugaban kasa baya kan yunkurin samar da zaman lafiya a kasar

Kungiyar matasan Tibi, TYC, ta marawa Shugaba Muhammadu Buhari baya game da matakan da ya dauka kan masu yunkurin ballewa daga kasa, musamman sake kama shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da samamen da DSS ta kai gidan Sunday Igboho, Leadership ta ruwaito.

Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Mike Msuaan, ta ce rashin daukan kwararan matakai a kan masu yunkurin ballewa daga Nigeria zai kara dilmiya kasar cikin matsaloli ne fiye da yadda ake zato.

Kara karanta wannan

Abdulsalami ya ja kunnen ‘yan siyasa da cewa sauya sheka ka iya haddasa husuma

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: Leadership
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kano: Ɗalibi ya cinnawa kansa wuta saboda bai samu kuɗin biyan jarrabawar NECO ba

Leadership ta ruwaito cewa Mr Msuaan ya jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya, musamman ta hanyar amfani da hanyar diflomasiyya don sake kama Kanu, hakan ya jadadawa yan Nigeria cewa shugaban kasa ba zuba wa bata gari da masu son ballewa daga kasa ido ya ke yi ba.

Kungiyar ta kara da cewa:

"Muna farin cikin kiran kan mu yan Nigeria ganin yadda gwamnatin kasar ta kama Mr Nnamdi Kanu ta dawo da shi bayan ya dade yana baza kalamai na tada rikici a kafafen watsa labarai."

Kungiyar ta kuma yaba da kokarin hukumomin tsaro bisa rawar da suke takawa domin kare martaba da mutuncin Nigeria ta hanyar dakile duk wasu bata gari da ke neman adabar mutanen kasar.

KU KARANTA: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Kara karanta wannan

Ba za mu iya yin galaba kan ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da tsofaffin makamai ba: Janar Irabor

Har wa yau, kungiyar ta yi tir da yadda Mr Kanu ya saba dokokin belin da aka bashi kafin ya tsere wanda hakan lamari ne da ya zama abin kunya da kaskanci ga gwamnatin tarayya.

"Amma, gwamnatin tarayya ta bawa yan Nigeria tabbacin cewa za a yi adalci kuma gashi yanzu ta cika alkawarrin.
"Babu kasar da za ta nade hannu tana kallon yan ta'adda da masu son raba kasa suna gina sojoji da barazana ga tsaro da zaman lafiya. Kama Kanu da sauran matakan da gwamnati ta dauka don samar da zaman lafiya abu ne da kowa ya kamata ya goyi baya," kungiyar ta kara da cewa.

Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Rahoton da The Guardian ta wallafa ya nuna cewa Hukumar yan farin kaya DSS tana farautar dan gwagwarmayar mai neman kafa kasar Yarbawa da aka fi sani da Sunday Igboho ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bayyana adadin mutanen da aka kashe daga shekarar 2011 zuwa 2021

Hukumar ta DSS ta sanar da hakan ne a daren ranar Alhamis 1 ga watan Yuli yayin taron manema labarai inda ta tabbatar cewa tawagar jami'an tsaro sun kai samame gidan Igboho da ke Soka a Ibadan, jihar Oyo.

An fahimci cewa cewar yan sandan sirrin na Nigeria sun tabbatar da cewa sun bindige mutum biyu cikin masu aiki tare da Igboho yayin da sauran aka ci galaba a kansu aka kama su kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel