Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a

Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a

  • Wani tsohon faifan bidiyo na marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan Jaafar Jaafar ya yada shi
  • A cikin bidiyon, an ga Shagari yana kunnawa tare da zukar sigari a lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama’a
  • Mutane da yawa ba su yarda sun sha mamaki, suna cewa har Shagari ya iya shan sigari lokacin da ake wa jama’a jawabi

Wasu kuma sun ce babu laifi a cikin abin da Shagari ya yi saboda ba laifi ba ne a sha sigari a bainar jama'a a zamanin baya

Wani tsohon faifan bidiyo na marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga jama’a a shekarun 1960 ya bayyana a shafukan sada zumunta.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a
Shagari yana zukar sigari a lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama’a Hoto: Jaafar Jaafar
Asali: Facebook

A cikin bidiyon da Jaafar Jaafar ya yada a Facebook, Balewa ya yi jawabi ga jama’a game da nuna wariyar launin fata kamar yadda wasu maza biyu suka mara masa baya, yayin da Shagari da wasu biyu suka zauna a layin baya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Da yake wallafa bidiyon, Jaafar ya rubuta:

"Duba karfin hali!

"Marigayi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari (hagu, layin baya) ya kunna sigari yayin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga masu sauraro a shekarun 60s."

Mutane da dama sun yi martani ga bidiyon

Bamaiyi An'iko Dabai ya ce:

"A wancan zamanin, ba laifi ba ne kuma kamar yadda kuke gani babu wanda ya damu da hakan."

Umar Dansuleiman II yayi tsokaci:

"Wannan rashin ladabi ne da kuma halin rashin nagarta ba karfin zuciya bane ..... Mutumin da ke da alhakin kula da hakkin wasu a bainar jama'a ...."

Maniru Ibrahim Dantitti ya rubuta:

"Allah ya yi masa rahama. Allah ya sanya shi a Aljannatul firdaus."

Umar Usman ya ce:

"Shan sigari a lokacin a yayin jawabi ba wani babban abu bane a zamanin da, ku duba hira da Ojukwu za ku gan shi yana shan sigari a kyamara yayin amsa tambayoyi."

Kara karanta wannan

Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi

Saleem Ahmed Imam ya ce:

"Abin kunya da rashin da'a."

Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce

A wani labarin, wani tsohon hoto na Shugaba Buhari yana more rayuwa lokacin da yake matashi ya haifar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.

Wani ma’abocin amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ya dimauta yanar gizo da wani hoto wanda ba kasafai ake gani ba na Shugaba Buhari yayin da wani saurayi yake rawa da wata farar mace ba takalmi.

Da yake wallafa hoton, ya rubuta cewa:

"PMB ya kasance dan sharholiya sosai yayin da yake tasowa. A zamanin nan, ya kame kansa !!! Dube shi yana shanawa a wani liyafa lokacin da yake saurayi !!!!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel