Da Duminsa: An Yi Awon Gaba da Matar Sunday Igboho Bayan Kame Nnamdi Kanu

Da Duminsa: An Yi Awon Gaba da Matar Sunday Igboho Bayan Kame Nnamdi Kanu

  • Wasu 'yan bindiga da ba gano su waye ba sun yi awon gaba da matar Sunday Igboho mai fafutukar kafa kasar Yarbawa
  • Rahoto ya bayyana cewa, an hallaka mutane bakwai a gidan nasa kafin daga bisa aka tattara matar da wasu mutane da dama
  • Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyu da kame mai rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu

Matar mai fafutukar kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ta shiga hannun ‘yan bindiga da suka kai hari gidansa da safiyar ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne kamar yadda shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyin cin gashin kai na Yarbawa, Ilana Omo Oodua, Emeritus Farfesa Banji Akintoye ya fada.

Ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma Manajan Sadarwar kungiyar, Mista Maxwell Adeleye ya gabatar wa manema labarai, Punch ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Wata Kungiyar Igbo Ta Bukaci Kasar Burtaniya Ta Sa Baki Kan Kame Nnamdi Kanu

Da Duminsa: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Sunday Igboho Mai Ikirarin Ballewa Daga Najeriya
Mai fafutukar kare kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Jawabin an yi masa taken, ‘Kasar Yarabawa: Wasu Sojojin Najeriya, Tare da rakiyar 'Yan Ta’addan Kasa da Kasa da Gwamnatin Najeriya ta dauki hayarsu, sun kai hari gidan Sunday Ighoho - Akintoye.’

A cewar Manajan Sadarwa, Akintoye ya yi zargin cewa:

"Maharan duk suna sanye da kayan sojoji kuma suna magana da Faransanci."

Ya ci gaba da cewa:

"'Yan bindigar sun kashe mutane bakwai a cikin gidan sannan suka tasa matar Igboho da wasu da dama daga wurin a gaba."

Lamarin ya faru ne awanni 72 kafin taron Yarbawa wanda za a yi ranar Asabar a Legas wanda Akintoye da Igboho za su halarta.

KARANTA WANNAN: Bayan Zarge-Zargen PDP Cewa APC Na Shirya Manakisa, APC Ta Mayar da Martani

Rahotanni Sun Bayyana Yadda Aka Kamo Nnamdi Kanu a Wata Kasar Turai

A wani labarin, Wani rahoto na jaridar Daily Sun ya nuna cewa an kama Mazi Nnamdi Kanu a Jamhuriyar Czech.

A cewar rahoton, shugaban IPOB ya yi tafiya daga kasar Ingila zuwa Singapore saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba kafin ya tafi Jamhuriyar Czech a ranar Juma’ar da ta gabata, 25 ga Yuni.

Rahoton ya ambato wata majiya, inda ya ce akwai wani bayani da jami'an Jamhuriyar Czech suka ba gwamnatin Najeriya, wanda ya kai ga kame Kanu a birnin Prague.

Asali: Legit.ng

Online view pixel