Da duminsa: Rashin aikin yi da talauci ke ruruta Boko Haram, in ji Shugaba Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, rikicin Boko Haram a Arewacin Najeriya galibi na haifar da rashin aikin yi na matasa da talauci, Punch ta ruwaito.
Buhari ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Arise TV wanda aka watsa a yau Alhamis 10 ga watan Yuni.

Asali: Original
Shugaban na Najeriya ya ce ya yi imanin cewa gwamnatinsa ta yi abubuwa da yawa don yaki da 'yan ta'adda amma matsalar da ke yankin "Arewa maso Gabas na da matukar wahala."
Ya ce gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya fada masa cewa, yawancin 'yan kungiyar ta Boko Haram 'yan Najeriya ne.
Karin bayani nan gaba...
Asali: Legit.ng