Muna tattaunawa da yan bindiga, ba zamu biya kudin fansa ba: Gwamnatin Neja

Muna tattaunawa da yan bindiga, ba zamu biya kudin fansa ba: Gwamnatin Neja

Mataimakin gwamnan Neja, Ahmed Ketso, ya bayyana cewa gwamnatin jihar na tattaunawa da yan bindigan da suka sace daliban makarantar Islamiya a jihar.

Yan bindiga sun kai hari makarantar Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegine, karamar hukumar Rafi a ranar Lahadi.

Yan bindigan sun yi awon gaba da sama da dalibai 100.

A cewar kamfanin dillancin labarai NAN, Ketso wanda yayi hira da manema labarai a Minna ranar Laraba, ya jaddada cewa ba zasu biya kudin fansa ba.

Ketso ya kara da cewa gwamnati na sane da tattaunawan da iyaye ke yi da yan bindiga.

Mataimakin gwamnan ya kara da cewa gwamnati ta fara tattauna da yan bindigan.

Yace, "Gwamnatin jihar Neja na tattaunawa don sakin wadannan dalibai, kuma muna da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba, za'a mayar da daliban wajen iyayensu."

"Gwamnati na tattaunawa da iyayen yaran. An tabbatar musu za'a dawo musu da yaransu."

Muna tattaunawa da yan bindiga, ba zamu biya kudin fansa ba: Gwamnatin Neja
Muna tattaunawa da yan bindiga, ba zamu biya kudin fansa ba: Gwamnatin Neja
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel