Yanzu-yanzu: An bindige shugaban hukumar NECO har lahira

Yanzu-yanzu: An bindige shugaban hukumar NECO har lahira

Punch na ruwaito cewa wasu yan bindiga da ake zargin makasa ne sun kashe shugaban hukumar shirya jarabawan NECO, Farfesa Godswill Obioma.

An hallaka Obioma ne daren Litinin a gidansa dake Minna, babbar birnin jihar Neja.

Uwargidar marigayin, Mrs Elizabeth Obioma, ta bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun shiga gidan sun hallakashi ba tare da daukan komai ba.

Obioma dan asalin jihar Abia ne.

Shekara daya kenan da Buhari ya nadashi matsayin Rijistan NECO a Mayun 2020.

Yanzu-yanzu: An bindige shugaban hukumar NECO har lahira
Yanzu-yanzu: An bindige shugaban hukumar NECO har lahira
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel