Salon Mulkin Buhari Ne Zai Tarwatsa Najeriya, Tsohuwar Minista Ta Caccaki DSS

Salon Mulkin Buhari Ne Zai Tarwatsa Najeriya, Tsohuwar Minista Ta Caccaki DSS

- Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, ta maida zazzafan martani ga hukumar tsaro ta DSS, tace hukumar ta tuhumi shugaba Buhari

- A jiya ne dai DSS ta bayyana cewa masu sukar shugaban ƙasa Buhari na shirin tarwatsa Najeriya

- A martanin data yi a shafinta na tuwita, tsohuwar Ministar tace ba wanda ke barazana ga kasancewar Najeriya tsintsiya ɗaya sama da shugaban ƙasa, wanda ayyukansa da halin ko inkula suka nuna haka

Tsohuwar ministan ilimi, Oby Ezekwesili, ta maida martani ga hukumar tsaro DSS kan cewa masu sukar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na shirin tarwatsa Najeriya.

KARANTA ANAN: Minista Ya Bayyana Matakin da Yakamata a Ɗauka Kan Gwamnonin da Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashi

A cewar tsohuwar ministar, babu wanda ke son tarwatsa Najeriya face salon mulkin shugaba Buhari da halin ko inkula da yake nunawa, shine babban abinda zai tawatsa Najeriya.

Ozekwesili ta bayyana haka ne a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Lahadi hukumar DSS ta bayyana masu sukar shugaba Buhari da marasa ɗa'a Kuma ta zargesu da barazana ga zaman Najeriya tsintsiya ɗaya.

Salon Mulkin Buhari ne Zai Tarwatsa Najeriya, Tshohuwar Minista ta Caccaki DSS
Salon Mulkin Buhari ne Zai Tarwatsa Najeriya, Tshohuwar Minista ta Caccaki DSS Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wasu yan Najeriya na ganin gazawar shugaba Buhari wajen shawo kan lamarin tsaron ƙasar nan, musamman wajen magance yan ta'addan Boko Haram, Satar mutane, da kuma yan bindiga a faɗin ƙasar.

DSS tace: "Muna Allah wadai da kalaman wasu mutane marasa ɗa'a waɗanda ke cigaba da zama barazana ga gwamnati da kuma kasancewar Najeriya ɗaya."

KARANTA ANAN: Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya

Yayin da take martani kan wannan kalaman na hukumar DSS a shafinta na kafar sada zumunta Tuwita, Oby Ezekwesili, ta ce:

"Kamata yayi DSS ta tura wannan kalaman nata kai tsaye ga shugaba Buhari, wanda shine mai kula dasu."

"Babu wani mutum ɗaya a Najeriya dake son jefa ƙasar cikin matsaloli ko barazanar kasancewar ƙasar tsintsiya ɗaya sama da shugaban ƙasa, wanda ayyukansa, da rashin kulawarsa ke ƙara barazana ga kasancewar Najeriya ɗaya.

"Saboda haka ina rokon ku DSS ku tuhumi shugaban ku amma ba wasu yan Najeriya ba."

A wani labarin kuma Ku Kawar da Mulkin APC Idan Baku Gamsu Ba Da Shi Ba, Gwamnan APC Ya Baiwa Matasa Shawara

Shekaru kaɗan suka rage babban zaɓen 2023 ya iso amma gwamna Fayemi ya shawarci matasa su fara aiki tun kafin zuwan zaɓen.

Gwamnan Ekiti yace maimakon damuwa da yawan ƙorafi, duk wadanda basa goyon bayan mulkin APC zasu iya haɗa kansu su kawar da ita a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel