Labari da ɗumi-ɗumi: ISWAP na kai hari a Kanamma a jihar Yobe

Labari da ɗumi-ɗumi: ISWAP na kai hari a Kanamma a jihar Yobe

Mayakan kungiyar ta'addanci ta Islamic State West Africa Province (ISWAP) ta kai hari a wani gari da ake kira Kanamma a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Nigeria, rahoton HumAngle.

Kanamma wadda ke kusa da kan iyakar Nigeria da Jamhuriyar Nijar ne babban gari a karamar hukumar Yunusari kuma wurin da yan Taliban na Nigeria suka zauna a farko da tsakiyar shekarun 2000, kafin Boko Haram ta bulla.

DUBA WANNAN: 2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

Labari da dumi-dumi: ISWAP na kai hari a Kanamma a jihar Yobe
Labari da dumi-dumi: ISWAP na kai hari a Kanamma a jihar Yobe
Asali: Original

Rundunar sojojin Nigeria tana da sansani da dakaru a garin na Kanamma.

KU KARANTA: 2023: An ƙaddamar da ƙungiyar goyon bayan Saraki a Daura

Wasu mutanen garin Geidam da suka bar gidajensu saboda hare-haren yan ta'adda sun tafi garin na Yunusari domin tsira da ransu.

Ku dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel