Da duminsa: Yan bindiga sun sake bindige dalibai 2 cikin wadanda suka sace a jami'ar Greenfield Kaduna

Yan bindiga masu garkuwa da mutanen da suka sace dalibai a jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna sun sake bindige biyu cikin kimanin dalibai 22 da suka sace.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta tsinci gawawwakin daliban ne cikin daji.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake ranar Litinin.

Wannan na faruwa ne kwanaki uku bayan yan bindigan sun kashe dalibai uku cikinsu.

Da duminsa: Yan bindiga sun sake bindige dalibai 2 cikin wadanda suka sace a jami'ar Greenfield Kaduna
Da duminsa: Yan bindiga sun sake bindige dalibai 2 cikin wadanda suka sace a jami'ar Greenfield Kaduna
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel