Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun sake sakin mutum 5 cikin daliban Afaka Kaduna

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun sake sakin mutum 5 cikin daliban Afaka Kaduna

Labari da duminsa na nuna cewa an sake sakin wasu dalibai biyar cikin 39 da aka sace a makarantar FCFM Afaka, jihar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan mutum biyar da aka saki ranar Litinin.

Adadin daliban Afaka da aka saki yanzu ya zama 10, har yanzu akwai sauran 29 hannun yan bindiga.

Daya daga cikin iyayen daliban ya bayyanawa TheNation cewa yan sanda sun dauki daliban a karamar hukumar Giwa.

Ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa Kaduna yanzu haka.

Mutumin yace: "Haka, an saki biyar cikin yaranmu. Yanzu haka muna sauraron isowarsu Kaduna."

"Ina tabbatar da muku cewa yan sanda sun daukesu. Amma bamu gansu ba har yanzu."

"Idan sun iso za'a kai su asibiti domin duba lafiyarsu, amma muna jiransu tukun."

Yayinda Legit Hausa ta tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, yace zai yi tsokaci kan lamarin nan ba da dadewa ba.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun sake sakin mutum 5 cikin daliban Afaka Kaduna
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun sake sakin mutum 5 cikin daliban Afaka Kaduna
Source: Twitter

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel