Yanzu-yanzu: Sanata ta tsallake rijiya da baya, an kashe mutum 3 yayin zabe a Ekiti

Yanzu-yanzu: Sanata ta tsallake rijiya da baya, an kashe mutum 3 yayin zabe a Ekiti

Akalla mutum uku sun rasa rayukansu a Ekiti ranar Asabar yayinda rikici ya barke lokacin da ake gudanar da zaben cike gibin kujerar dan majalisar dokokin jihar na mazabar Ekiti East.

Ana gudanar da zaben ne domin maye gurbin kujerar dan majalisar All Progressives Congress (APC), Juwa Adegbuyi, wanda ya mutu.

TVC ta ruwwaito cewa an fara zaben cikin kwanciyar hankali amma abubuwa suka rikice lokacin da wasu yan bangan siyasa suka fara harbin bindiga.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa yan bindigan sun bulla cikin jama'a kawai suka fara harbon kan mai uwa da wabi domin fitittikan mutane da jami'an zabe.

Ya yi bayanin cewa yan bindigan sun bude wuta a gunduma ta 007 inda Sanata Biodun Olujimi ya kada kuri'arta kuma ta tsallake rijiya da baya.

A cewarsa, wata yar sanda dake rumfar zaben ta rasa rayuwarta a take yayinda sauran mutum biyu suka mutu a asibitin Omuo-Ekiti inda aka garzaya da su.

Yanzu-yanzu: Sanata ta tsallake rijiya da baya, an kashe mutum 3 yayin zabe a Ekiti
Yanzu-yanzu: Sanata ta tsallake rijiya da baya, an kashe mutum 3 yayin zabe a Ekiti Photo credit: @Biodun_Olujimi/Twitter, Nigerian Tribune
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel