Da dumi-dumin: Daga karshe, Kotu ta baiwa Mahdi Shehu, beli

Da dumi-dumin: Daga karshe, Kotu ta baiwa Mahdi Shehu, beli

Babban kotun tarayya dake Kano ta baiwa dan kasuwa kuma mai tonon silili Mahdi Shehu beli bayan kin amsa laifin abubuwa shida da gwamnatin jihar Katsina ke zarginshi da su.

Daily Trust ta rahoto cewa alkali mai shari'a, Ambrose Lewis Allagoa, ya ce kada a sakeshi tukun sai ya cika sharrudan belin.

An bashi belin milyan 10 kuma wani mazaunin jihar Kano mai dukiya ya tsaya masa.

An dage karar zuwa ranar 19 ga watan Mayu don cigaba da sauraron karan.

Gwamnatin jihar Katsina ya shigar da Mahdi Shehu kotu kan zargin almundahana da almubazzarancin da yayi wa gwamna Aminu Bello Masari.

Da dumi-dumin: Daga karshe, Kotu ta baiwa Mahdi Shehu, beli
Da dumi-dumin: Daga karshe, Kotu ta baiwa Mahdi Shehu, beli
Source: Twitter

Source: Legit

Tags:
Online view pixel