Gungun ‘Yan bindiga sun sace mutane 7 a hanya, har da ‘Dan Jariri mai shekara 1 da haihuwa

Gungun ‘Yan bindiga sun sace mutane 7 a hanya, har da ‘Dan Jariri mai shekara 1 da haihuwa

- ‘Yan bindiga sun sake dura yankin Takum-Wukari, sun sace wasu fasinjoji

- An tare wata mota da ta dauko mutane daga Takum za ta tafi garin Wukari

- Wannan ne karo na biyu a 2021 da aka yi garkuwa da matafiya daga Takum

Akalla ‘yan bindiga 10 ne ake zargin sun tare wani titi a kusa da garin Chanchangi, a hanyar Takum zuwa Wukari, jihar Taraba, su ka sace mutane.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 8 ga watan Maris, 2021, da maraice bayan wata mota ta dauko fasinjoji.

‘Yan bindigan sun tursasa wannan mota da ta ke dauke da fasinjoji 10 da nufin zuwa Wukari daga Takum ta shiga cikin kungurmin jejin da ke yankin.

Maiwada Takum, wani daga cikin ‘yanuwan matafiyan, ya shaida wa ‘yan jarida cewa ‘yan bindigan sun tsare mutane bakwai, sun yi garkuwa da su.

KU KARANTA: Gumi: Ka iya bakin ka - Sojoji

Majiyar ta bayyana cewa an dauke wani jariri mai shekara guda, an raba shi da mahaifiyarsa a motar.

Daga baya an tsinci wannan mota kirar ‘Sharon’ a cikin jejin Benuwai inda jihar Taraba ta yi iyaka da jihar Arewa maso tsakiyar ta yankin garin Chanchangi.

Maiwada ya sanar da manema labarai cewa tun da aka yi gaba da wadannan mutane har zuwa yanzu, ‘yan bindigan ba su tuntubi iyalansu ta waya ba.

Mahaifiyar da aka dauke wa jariri ta na cikin wani irin mawuyacin hali, yanzu haka an kwantar da ita a wani karamin asibiti da ke garin Takum, inji Maiwada.

KU KARANTA: Miyagun kwayoyi sun shiga fadar fitaccen Sarki a Najeriya

Gungun ‘Yan bindiga sun sace mutane 7 a hanya, har da ‘Dan Jariri mai shekara 1 da haihuwa
‘Yan bindiga Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewarsa, wannan ne karo na biyu a cikin watanni uku da aka tare mutane a wannan titin daga garin Takum a kan hanyarsu ta zuwa garin Wukari, a jihar Taraba.

Mutane sun dura kan ‘Yan Sandan Najeriya a dalilin kama wasu mutane wadanda su ka cafke wani makaho da ake zargin ya na cikin jagoorin ‘Yan bindigan a Oyo.

Rundunar ‘Yan Sanda ta ce wadannan mutane da 'yan kungiyar OPC ne sun kashe wata mata da su ka kona gidan Wakiliin Ayete yayin da su ke kokarin cafke shi.

Kungiyar OPC ta na zargin Isiaku Wakiliin Ayete ya na da hannu a ta'adin da ake yi a Ibarapa.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel