Cike nike da farin ciki da labarin sakin daliban Jangebe, Shugaba Buhari

Cike nike da farin ciki da labarin sakin daliban Jangebe, Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana farin cikin na samun labarin samun yancin daliban makarantar sakandaren GGSS Jangebe daga hannun yan bindiga.

Buhari ya ce cike yake da farin cikin dukkan dalibai matan sun dawo gida ba tare da wani matsala ko rashin ran ko mutum daya cikinsu ba.

Ya jaddada cewa gwamnatin na iyakan kokarin kawo karshen ire-iren wadannan sace-sacen na daliban makarantun kwana.

A jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita, Buhari ya ce jami'an Sojoji da na yan sanda zasu cigaba da kokarin dakile masu garkuwa da mutane.

"Ina taya iyalan da al'ummar jihar Zamfara murnar maraba da sakin daliban GGSS Jangebe. Wannan labari ya kawo min farin ciki matuka. Ina farin cikin wannan abu ya zo karshe ba tare da wani matsala ba." Buhari yace.

"Muna iyakan kokari wajen kawo karshen wadannan sace-sacen."

Cike nike da farin ciki da labarin sakin daliban Jangebe, Shugaba Buhari
Cike nike da farin ciki da labarin sakin daliban Jangebe, Shugaba Buhari Hoto: TVCNews
Source: Facebook

Source: Legit.ng

Online view pixel