Fulani Makiyaya da daukar bindiga: Ina nan akan baka na, Gwamnan jihar Bauchi

Fulani Makiyaya da daukar bindiga: Ina nan akan baka na, Gwamnan jihar Bauchi

Gwamna Bala na jihar Bauchi a ranar Juma'a ya kare kansa kan jawabin da yayi kan Fulani Makiyaya inda yace suna daukan bindiga AK-47 don kare kansu.

"Ishara ne da mutum keyi domin nuna muku irin halin da yake ciki da irin abubuwan da ake masa saboda ana mai kallon dan ta'adda, saboda haka kuma ya nada hakkin kare kansa," Gwamnan ya bayyana a hirarsa a shirin Sunrise na ChannelsTV.

"Mutumin Fulani kullum zaluntarsa akeyi, saboda ana masa kallon tsagera, kuma duk inda yaje, farautarsa ake yi. Ba a kudu maso yamma kadai ba ko kudu maso gabas kadai ba, har a Arewa saboda ana kwace masa dukiyarsa wato Shanu."

"Wani lokacin kuma a ci su tara saboda kawai shanu ya shiga gonar wani."

"Saboda haka bai da wata mafita illa ya kare kansa."

Fulani Makiyaya da daukar bindiga: Ina nan akan baka na, Gwamnan jihar Bauchi
Fulani Makiyaya da daukar bindiga: Ina nan akan baka na, Gwamnan jihar Bauchi
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel