Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, rasuwa

BBC na ruwaito cewa Allah ya yiwa tsohon shugaban hukumar kwastam ta ƙasa, Dikko Inde, rasuwar.

Rahoton ya nuna cewa majiya mai ƙarfi da ke da kusanci da mamacin ta tabbatar cewa ya rasu ne a Abuja bayan fama da rashin lafiya.

Dikko, wanda ya jagoranci hukumar kwastam daga shekarar 2009 zuwa 2015, na gurfana gaban kotu kan zargin rashawa.

An kwace dukiyoyi irinsu motoci, gidaje na biliyoyin naira.

An haifeshi ranar 11 ga Mayu, 1960, a garin Musawa, jihar Katsina, inda ya halarci makarantan gwamnati Government College Kaduna a 1974.

Ya shiga hukumar Kwastam a shekarar 1988.

Saurari karin bayani....

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, rasuwa
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel