Gaba da gabanta: An samu sabon Mai kudin Duniya bayan Elon Musk ya yi makonni 6 ya na tashe

Gaba da gabanta: An samu sabon Mai kudin Duniya bayan Elon Musk ya yi makonni 6 ya na tashe

- Jeff Bezos shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Duniya a yanzu haka

- Bezos ya dawo kan matsayin da yake rike da shi ne tun a shekarar 2017

- Hakan na zuwa ne bayan kamfanin Tesla ya jawowa Elson Musk asara

Mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos, ya koma kan matsayinsa na Mai kudin Duniya. Haka na zuwa ne bayan hannun jarin kamfanin Tesla sun girgiza.

CNN ta ce a sakamakon kasa da hannun jarin Tesla su ka yi da 2%, dukiyar Elon Musk ta yi kasa, inda Attajirin ya gamu da asarar fam Dala biliyan $4.6.

Wannan asara ce ta jawo Musk ya sauka daga matsayin na daya a alkaluman Bloomberg Billionaires Index na shahararrun masu kudin Duniya.

A daidai wannan lokaci kuma Bezos mai shekara 75 a Duniya ya dawo kan matsayin da yake kai, inda ake kiyasta dukiyarsa a kan akalla fam Dala biliyan 191.

KU KARANTA: Gudumuwar da Dangote ya bada domin a farfado da ilmi ta kai N10bn

A watan jiya ne Musk ya doke Bezos bayan ya ba Dala biliyan 185 baya. Bai wuce makonni shida ya na kan wannan kujera ba sai abokin hammayarsa ya doke shi.

Tun 2017 shugaban kamfanin na Amazon, Bezos ya zama mutumin da ya fi kowa kudi a ban kasa.

Shi kuwa Musk ya yi gaba ne a shekarar bara bayan da hannun jerin kamfaninsa na Tesla ya tashi da 743%, wannan ya sa ya samu sama da Dala biliyan 150.

Kwanakin baya Tesla ya saye kudin Bitcoins na fam dala biliyan 1.5. Dalilin wannan, kudin ya kara daraja, aka koma saida kowane bitcoins a kan fam $50, 000.

Gaba da gabanta: An samu sabon Mai kudin Duniya bayan Elon Musk ya yi makonni 6 ya na tashe
Bezos da Musk Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

KU KARANTA: Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

Masana su na ganin cewa ba za a dade ba mutumin kasar Afrika ta Kudun, Musk, zai sake doke Bezos.

Kwanakin baya mun kawo maku tarihin attajiran, inda ku ka ji cewa a lokacin shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos shi ne na biyu a sahun attajirai.

A wancan lokaci, dukiyarsa ta kai Dala biliyan 184. Bezos ya karaya kadan ne bayan ya saki mai dakinsa a 2019, wanda a sanadiyyar rabuwarsu, ta tafi da dukiyarsa.

Na ukunsu shi ne Bill Gates wanda ya fi kowa dadewa a sahun attajiran Duniya. Abin da shugaban kamfanin na Microsoft ya mallaka ya haura Dala biliyan 120.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel