Yanzu yanzu: Dan Maina, Faisal, ya tsere zuwa Amurka, EFCC ta fadawa kotu

Yanzu yanzu: Dan Maina, Faisal, ya tsere zuwa Amurka, EFCC ta fadawa kotu

- Faisal Maina, dan tsohon shugaban hukumar yin garambawul ga tsarin fansho, PRTT, Abdulrasheed Maina ya tsere zuwa Amurka

- Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ne ya shaidawa kotu hakan a zamanta na ranar Alhamis

- Ana tuhumar Faisal da mahaifinsa Abdulrasheed Maina da laifuka da dama da suka shafi almundahanar kudade

Faisal Maina, dan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar yin garambawul ga tsarin fansho, PRTT, ya tsere zuwa kasar Amurka, kamar yadda hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta shaidawa kotu.

Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, a ranar Alhamis, ya shaidawa Mai shari'a Okon Abang na babban kotun tarayya da ke Abuja, Vanguard ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara wa'azi a jihar

Yanzu yanzu: Dan Maina, Faisal, ya tsere zuwa Amurka, EFCC ta fadawa kotu
Yanzu yanzu: Dan Maina, Faisal, ya tsere zuwa Amurka, EFCC ta fadawa kotu. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

KU KARANTA: Allah ya yi wa kawun Sheikh Isa Ali Pantami rasuwa

Abubakar ya ce daga bayanan da ya samu daga hukumar yaki da rashawar, Faisal, ya sulale daga Jamhuriyar Nijar ya tafi kasar Amurka.

Tunda farko, a zaman na ranar Alhamis, Mai sharia Abang, yayin zaman kotu ya umurci wanda ya karbi belin Faisal, Hon Sani Dan-Galadima mai wakiltar Kaura-Namoda daga jihar Zamfara ya mika kadarar da ya bada a matsayin jingina.

Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito cewa an bada belin Faisal ne kan kudi Naira miliyan 60 tare da wanda zai tsaya masa kuma ya kasance dan majalisar wakilai mai ci.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel