Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar wakilan tarayya

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar wakilan tarayya

Rikici ya barke yanzu haka a daki na 028, inda aka shirya taron tattaunawa da jama'a kan dokar kamfanin man fetur PIB tsakanin wasu da suka halarci zaman.

Rahoton Vanguard ya bayyana cewa har yanzu ba'a gane wadanda suka tada rikicin ba amma ana kyautata zaton wasu yan jihohin Neja Delta ne.

Rikicin ya barke misalin karfe 12:10 na ranar lokacin da shugaban kwamitin, Hanarabul Mohammed Munguno, yayi kira ga yan jihohin Neja Deltan su gabatar da jawabinsu.

Kawo yanzu, yan majalisa da sauran wadanda ke hallare a wajen sun gudu daga dakin.

Karin bayani na nan tafe...

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar wakilan tarayya
Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar wakilan tarayya
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel